Home Back

Malaman Musulunci Sun Yi Hannun Riga da Limami Kan Bijirewa Basarake, Sun Ba da Shawara

legit.ng 2024/7/16
  • Yayin da ake rikici tsakani basarake da babban limamin gari, gamayyar malaman Musulunci sun tsoma baki
  • Kungiyar malaman Musulunci a Ogbomoso da ke jihar Oyo ta kalubalanci Sheikh Taliat Yunus kan bijirewa umarnin Oba Afolabi Ghandi
  • Hakan ya biyo sabanin da limamin ya samu da basaraken kan zuwa aikin hajji ba tare da izninsa ba wanda ya jawo rudani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gamayyar limamai da malaman Musulunci a Ogbomoso sun soki limamin masallacin garin kan rigimarsa da Oba Afolabi Ghandi.

Malaman sun zargi Sheikh Taliat Yunus da rashin biyayya ga basaraken kan halartar aikin hajji babu izininsa.

Kungiyar ta bayyana haka ne a jiya Asabar 29 ga watan Yunin 2024 yayin ganawa da manema labarai a Ogbomoso, Tribune ta tattaro.

Sun bayyana abin da limamin ya yi da cewa ba rashin daraja Oba na Ogbomoso kadai ya yi ba har ma da sarautar gargajiya a jihar.

Malaman sun kara da cewa a Musulmai a garin ba za su taba barin wani ya taba martabar basaraken ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A martaninsa, Balogun Musulumi, Alhaji Bello Ayobami ya ce Musulmai ba za su taba bari wasu su jawo rashin jituwa a Ogbomoso ba.

Ayobami ya ce tun shekarar 1818 nadawa da sauke limamin Ogbomoso na hannun basaraken garin tun asali.

Ya ce shekaru da dama ba a taba samun sabani a Ogbomoso ba duk da bambance-bambancen addinai a garin.

Har ila yau, ya ce Oba Afolabi ya na da ikon naɗa duk limamin daya ga dama daga kowane gidan Musulmai a Ogbomoso.

Basarake ya dauki mataki kan babban limami

Kun ji cewa Oba na Ogbomoso, Afolabi Ghandi ya kalubalanci babban limamin garin Sheikh Taliat Yunus kan bijirewa umarninsa.

Basaraken ya caccaki shehin malamin kan zuwa aikin hajji a Saudiyya ba tare da sanar da shi ba kamar yadda aka yi yarjejeniya.

Asali: Legit.ng

People are also reading