'Yan Sanda Sun Bankado Sababbin Dabarun Kwacen Babura, An Fargar da Matuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun- Karuwar rahotannin kwacen babura a jihar Osun ya tilasta rundunar 'yan sandan daukar matakin sanar da jama'a sabon dabarar barayin da ke kwacen.
Rundunar ta gargadi masu sana'ar cewa an gano miyagun na tare masu babura, sai su ja su lungu inda a nan ne su ke tilasta masu rabuwa da babura ba tare da an gansu ba.
Vanguard News ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Yemisi Opalola ya gargadi masu babura da su sanya idanu kan irin fasinjojin da su ke dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Osun ta bayyana cewa an samu karuwar rahotannin kwacen babura a fadin jihar.
Kakakin ya gargadi masu sana'ar tuka babura da su lura da fasinjojin da ke neman a kai su loko musamman idan sawu ya dauke, domin a nan aka fi yin ta'asar.
Peoples Gazzette ta wallafa cewa an gano barayin da ke badda-bami a matsayin fasinjoji na yi wa masu baburan tayin kudin da ba sa iya kin daukarsu.
A wani labarin kun ji cewa an shiga zaman dar-dar bayan wasu sojojin ruwa sun yi sanadiyyar mutuwar jami'in dan sanda a unguwar Okokomaiko da ke jihar Legas.
Jami'an hulda da jama'a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da rasuwar jami'in mai matsayin sufeto inda ya ce ya yanke jiki ya fadi, kuma an tabbatar da rasuwarsa.
Asali: Legit.ng