Home Back

Mata ‘yan ƙunar-baƙin-wake sun tashi bama-bamai kan ‘yan bidirin buki, cikin maƙabarta da wasu wurare biyu

premiumtimesng.com 5 days ago
Neman aure ya yi sanadiyyar mutuwar Nabajallah, kasurgumin dan bindiga a Katsina

Wasu mata huɗu da aka haƙƙaƙe cewa ‘yan Boko Haram ne, sun tashi bama-baman ƙunar-baƙin-wake a wurare daban-daban a Jihar Barno.

Cikin mutanen da aka kashe har da wani soja ɗaya, a harin wanda aka kai har kan taron ‘yan shagalin bukin ɗaurin aure a Mararaban Gwoza.

“Hari na biyu kuwa an kai shi ne kan wani shingen jami’an tsaro, har aka kashe wani soja da fararen hula biyu.” Haka majiya ta shaida.

Majiyar ta ƙara da cewa harin ƙunar baƙin wake ya uku kuwa an yi ne kan kantinan hada-hadar zamani, wato shopping mall, sai kuma na huɗu a filin maƙabarta.”

Ya ce an kai hare-hare na huɗu a filin wata maƙabarta tsakanin ƙarfe 3 na yamma zuwa ƙarfe 5 na yamma, duk a ranar Asabar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Barno, CP Yusuf Lawal, ya tabbatar da afkuwar lamarin, kuma ya ce mutum shida ne aka kashe, yayin da wasu mutum 17 suka ji ciwo, kuma ana ba su kulawar da ya dace a asibiti

An ce waɗanda suka kai harin duk yaran wani gogarman Boko Haram mai suna Ali Ngulde ne.

People are also reading