Fitaccen Jarumin Nollywood, Olu Jacobs Ya Rigamu Gidan Gaskiya?
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ana fargabar Nollywood ta sake yin rashin daya daga cikin tsofaffin jarumanta kamar yadda wani rahoto ya bayyana cewa fitaccen jarumi Oludotun Baiyewu Jacobs ya rasu.
Rahotannin rasuwar jarumi Olu Jacobs sun karade shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni wanda ya haifar da martani daga masu amfani da yanar gizo.
Jaridar Tribune ta tattaro cewa Olu Jacobs, wanda da yawan matasa suka taso suna ganinsa a talabijin ya rasu kwanaki kadan da cikarsa shekaru 83 a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, a wani martani da matarsa Joke Silva ta yi, ta ce labaran da ake yadawa na mutuwar mijinta ba gaskiya ba ne domin har yanzu Olu Jacobs yana nan da ransa.
Da take magana da jaridar PM News a yammacin yau Lahadi, Joke Silva ta karyata jita-jitar, tana mai cewa "mijinta yana raye kuma yana samun sauki sosai."
Wannan dai shi ne karo na biyu da jita-jita game da mutuwar fitaccen jarumin, wanda ainihin sunansa Oludotun Baiyewu Jacobs, ke ta yawo a shafukan sada zumunta.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da masoyansa da ma masu kallon fina-finan Nollywood suka yi kan rasuwar jarumin.
capry_sunn:
"Sai mutuwa za ta raba mu" lallai Joke Silver ta rike wannan alkawarin."
comfort_gabriella1:
"Joke silver ta tsaya masa har mutuwa ta rabasu, aure nagari kenan, Allah ya sa ya huta."
b_uniqu.e:
"Matarshi ta zauna dashi har karshen rayuwarsa, Madam Joke silver abar alfahari ce, Allah ya sa ya huta."
ibrolee___:
"Ya samu mata 'yar amana, ta tsaya masa har zuwa karshen rayuwarsa."
A wani labarin, mun ruwaito cewa Jarumar Nollywood, Stella Ikwuegbu ta rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni.
An bayyana cewa Stella ta mutu ne sakamakon ciwon daji da ya cinye kafarta kuma mutuwarta ta jefa mutane cikin jimami.
Asali: Legit.ng