Home Back

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Tana Kasa Tana Dabo

leadership.ng 2024/6/26
Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Tana Kasa Tana Dabo

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya sauka a Katar domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar a Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su wadda a yanzu haka take kasa take dabo tun bayan martanin kungiyar Hamas.

Rahotanni dai sun ce tun tsakar dare mista Blinken ya farka daga barci yake ta nazarin sakon da Hamas ta mika wa Katar da Egypt masu shiga tsakani.

Kungiyar Hamas dai ta ce a shirye take ta yi maraba da yarjejeniyar to amma ta sa sharadin cewa sai idan Isra’ila ta amince da dakatar da yaki baki dayansa.

Gwamnatin Isra’ila dai ba ta mayar da martani ba amma kuma wani jami’in Isra’ilar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya ce sauyin da Hamas ke son yi ga yarjejeniyar tamkar watsi da ita ne.

BBC na daga cikin tawagar ‘yan jaridar da ke tafiya da mista Blinken a ziyarar tasa zu-wa Birnin Doha inda yake ganawa da shugabannin Katar domin tabbatar da yarjejeni-yar ba ta samu cikas ba.

A ranar Talata dai Mista Blinken da firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu sun kara nanata muhimmancin yarjejeniyar duk da cewa Mista Netanyahu bai fito fili ya yi maraba da yarjejeniyar ba wadda shugaban Amurka, Joe Biden ya ce Isra’ilar ce ta fito da ita.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Amurka, John Kirby ya ce ana duba martanin na Ha-mas. Kungiyar dai ta ce za ta hau teburin sulhu da zuciya daya.

“Mun karbi maratanin Hamas da ta gabatar ta hannun Katar da Egypt muna kuma nazartarsa yanzu haka kuma ina tunanin cewar iya abin da za mu iya yi kenan yanzu, tun da mun sami wannan martanin a hannun yanzu, kuma za mu yi aiki a kansa,” in ji Kirby.

Wakiliyar BBC ta ce wani jami’in Hamas Aze Tariksh ya ce martanin na su ya bude kofar cimma yarjrjeniya.

To amma wani jami’in Isra’ila da ya nemi a sakaye sunansa ya zargi Hamas da sauya wasu muhimman sassa na daftarin yarjejeniyar, kuma haka a wajensu, tamkar ta yi watsi da yarjejeniyar ne.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta ce amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi, wani mataki ne na goyon bayan samar da zaman lafiya.

Linda Thomas-Greenfield ta ce kasashen duniya sun hada kai kan yarjejeniyar da za ta ceci rayuka, da mayar da mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su gida da kuma taimaka wa fararen hula Falasdinawa.

A rubuce dai kudurin na nuna cewa Isra’ila ta amince da yarjejeniyar wadda shugaba Biden ya sanar a watan jiya.

People are also reading