Home Back

Kwantan Abinci: Wani Bawan Allah Ya Ceto Aisha Mai Abinci Daga Tafka Asara a Bauchi

legit.ng 2024/10/5
  • Daga karshe, wani bawan Allah ya sayi abincin Hajiya Aisha wacce ta yi korafi kan yaudararta da ka yi ta dafa abinci mai yawa
  • Aisha ta nemi taimakon al'umma bayan wani ya ba ta kwangilar dafa abinci har na mutane 9,000 amma ba ta sake ganinsa ba
  • Hakan ya jawo mutane da dama suka tausaya mata inda suk a yi ta yada bidiyon domin samun wanda zai taimaka mata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Bayan korafin da wata mai siyar da abinci ta yi a jihar Bauchi, wani bawan Alkah ya sayi abincin gaba daya.

Matar mai suna Hajiya Aisha ta roki al'umma su taimaka mata bayan wani ba ta kwangilar dafa abinci har na mutane 9,000.

Wani mai suna Kwamred Ameen Sulaiman shi ya wallafa faifan bidiyon a shafin Facebook inda ya tabbatar an saye abincin gaba daya.

Ameen ya ce wani bawan Allah ne ya sayi abincin gaba daya inda ya raba ga al'umma mabukata.

Sai dai bai bayyana sunan wanda ya taimaki baiwar Allan ba yayin da wasu ke rade-radin cewa gwamnatin jihar Bauchi ne ta sayi abincin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading