Home Back

Tinubu shugaba ne mai gaggauta ɗaukar matakan gaggawa – Nuhu Ribadu

premiumtimesng.com 2024/5/15
Tinubu shugaba ne mai gaggauta ɗaukar matakan gaggawa – Nuhu Ribadu

Nuhu Ribadu, Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa irin matakan gaggawa da Shugaba Tinubu ke ɗauka wajen magance matsalolin tsaro su na haifar da ɗa mai ido sosai.

Ribadu ya yi wannan bayani a ranar Alhamis, lokacin da ya ke gabatar da takardar Babban Baƙo mai jawabi a yayin lacca, a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Ya ce, shirin gwamnatin Tinubu na “Fata Nagari Lamiri” (Renewed Hope Agenda), ya samar da cikakken tsare-tsare da matakan daƙile matsalar tsaro.

Maƙalar mai taken: Hanyoyin Shawo Kan Ƙalubalen Matsalolin Tsaro a Arewacin Najeriya”, Ribadu ya bayyana irin ci gaban da aka samu sakamakon gaggauta yin abin da ya dace a duk lokacin da dacewar gaggautawar ce ta dace.

Ya ce ƙalubale ne wanda ya shafi kowa, kuma kowa na ciki, shi ya sa ake haɗa hannu baki ɗaya ake kan samun nasara.

Ya ƙara da cewa yaƙi da matsalolin tsaro abu ne da ke tafiya kafaɗa da kafaɗa da sauran tsare-tsaren magance matsalolin da suka shafi fatara da talauci, rashin aikin yi, kawo ƙarshen ware wasu ba’arin ɓangarorin al’umma ta hanyar jawo su a jika, daƙile yawan tashe-tashen hankulan ƙabilanci ta hanyar ɗarsasa zaman lumana da yalwar arziki a Arewacin Najeriya.

Ya ƙara da cewa Tinubu ya na sane ya naɗa ‘yan Arewa manyan muƙaman da suka shafi harkokin tsaro, saboda ya shigar da mutanen da ke kusa da inda ake fama da ƙalubalen, domin a samu hanyoyin warware matsalolin sosai da sosai.

“Har yanzu dai da sauran rina a kaba. Ba mu kai ga fita daga waɗannan matsalolin ba tukunna, to amma kuma mun samu gagarumar nasara wajen rage yawan rayukan da ake salwantarwa. Sannan kuma muna ci gaba wajen hana muggan makamai isa hannun mugayen mutane.

“To amma kuma ci gaba da bijiro da hanyoyin amfani da sojoji, siyasa da inganta rayuwar al’umma za su ci gaba da taimakawa a samu nasarar amfani da sojoji.

Da ya ke bayanin rata, tazara da bambancin da ke tsakanin Arewa da Kudu, Ribadu ya kawo shawarar cewa akwai buƙatar a kai ɗauki sosai a wasu ɓangarorin da talauci da rashin aikin yi suka yi kaka-gida.

Ya kuma nuna damuwa dangane da yawaitar safarar muggan makamai a Arewacin Najeriya. Har ya yi nemi a haɗa ƙarfi wajen daƙile wannan mummunar sana’a.

People are also reading