Back to the last page

Tsuntsayen da ke da dabarar cire guba a jikin kwaɗi kafin cinye su

bbc.com 13 minutes ago
.

Asalin hoton, SUPPLIED

A Australiya tsuntsayen Jinjimi na daga cikin dabbobin da aka fi ƙyama a ƙasar.

Tsuntsun jinjimi ya shahara wajen hanyar da yake bi wajen farauto abincinsa a ko'ina ya same shi, ta hanyar shiga cikin kududdufi da fautar abinci a hannun mutane.

To amma da alama tsuntsun na ƙoƙarin sauya mummunar hanyar farautar abincinsa da aka san shi da ita.

Ya fara koyon yadda zai zaƙulo tare da cin kwaɗin da al'ummar ƙasar ke matuƙar ƙyama da ƙi saboda gubar da suke ɗauke da ita a jikin fatarsu.

Kwaɗin waɗanda suka fara bayyana a ƙasar a shekarun 1930, babu wata dabba da ke cin namansu, abin da ya sa yawansu ya zarta na sauran dabbobi a ƙasar.

Fatar kwaɗin na ɗauke da wani sinadarin guba, wanda kwaɗon ke saki da zarar wata dabba ta kai masa farmaki, lamarin da zai yi sanadiyyar mutuwar dabbar nan take sakamakon bugun zuciya.

Emily Vincent ta sha mamaki lokacin da al'ummar ƙasar suka fara wallafa hotuna da bidiyon tsuntsun yayin da yake wasa da kwaɗin.

Misis Vincent wadda ke gudanar da wasu shirye-shirye game da rayuwar dabobi a gidauniyar Watergum, ta ce wannan lamari ya bai wa mutane da dama mamaki musamman a gabashin ƙasar.

Ta shaida wa BBC cewa suna matuƙar mamakin yadda tsuntsayen na Jinjimin ke wasa da kwaɗin ta hanyar matse ruwan gubar da ke jikinsu.

Baya ga haka sukan binciko kwaɗin a duk wuraren da suke kamar cikin ruwa tare da zaƙulo kwaɗin a can ƙarƙashin ruwa''.

Ta ce lallai abin al'ajabi ne yadda tsuntsayen suka koyi yadda za su raba kwaɗin da gubar da ke jikin fatarsu kafin su cinye su. ''Abin akwai ban al'ajabi''.

Ba wannan ne karon farko da aka ga tsuntsaye na cin kwaɗin ba, kamar yadda Farfesa Rick Shine ya shaida wa BBC.

Guba ba ta faye yi musu illa ba, kamar sauran dabbobi irinsu macizai da kadoji.

.

Asalin hoton, SUPPLIED

To amma idan gubar ta yi musu yawa suna iya mutuwa, kamar yadda Farfesa Shine ya faɗa.

Yayin da kwaɗin suka yaɗu a fadin ƙasar Austariya, sauran tsuntsaye irin su shaho da hankaka ka iya koyo tare da sabawa da cin naman kwaɗin.

Sukan ɗauki kwaɗin tare da fyeɗe su domin cin naman kayan cikinsu, su bar sauran gangar jikin ba tare da sun taba shi ba.

Wannan shi ne karon farko da Farfesa Shine - wanda ya kwashe shekara 20 yana nazari a kan kwaɗi - ya taɓa jin wani tsuntsu na amfani da wannan hanyar wajen cin naman kwaɗin.

Hakan ya nuna cewa tsuntsaye ne masu basira da fasaha, in ji misis Vincent.

"Sukan tilasta wa kwaɗin rabuwa da gubar da ke jikinsu da kansu, ta hanyar matse kwaɗin har sai ruwan da ke ɗauke da gubar ya fice daga jikin fatar kwaɗin.

Farfesa Shine da Misis Vincent duka sun ce wannan wata alama ce da ke nuna yadda dabbobin ƙasar ke ƙoƙarin sabawa da kwaɗin, waɗanda a yanzu ake hasashen yawansu a ƙasar ya zarta biliyan biyu.

Sannu a hankali wasu dabbobin na gane yadda za su mu'amalanci kwaɗin 'waɗanda ba a farautarsu'.

Wasu na ganin cewa wasu dabbobin na samun sauyi ta fuskar halittarsu lamarin da ke sa raguwar illar guba a jikinsu.

Ga kuma tsuntsaye irinsu su Jinjimi waɗanda suka gano hanyar cin kwaɗin ba tare da wata illa ba.

Haƙiƙa hakan zai taimaka wajen kawo raguwar yawan kwaɗin a faɗin ƙasar.

Haka kuma akwai tsuntsaye irinsu su Jinjimi waɗanda suka gano hanyar cin kwaɗin ba tare da wata illa ba.

Inda hakan zai taimaka wajen kawo raguwar yawan kwaɗin a faɗin ƙasar.

.

Asalin hoton, Getty Images

Farfesa Shine ya ce tsuntsayen Jinjimi na ƙoƙari wajen rage yawan waɗannan nau'i na kwaɗi masu cike da hatsarin gaske a ƙasar.

"Waɗannan tsuntsaye na aiki kamar jami'an tsaro na ɓoye wajen rage yawan ƙwadin a duk shekara'', in ji Farfesa Shine.

Haƙiƙa muna godiya ga waɗannan tsuntsaye da a baya al'ummar Autraliya ke ƙyamata.

Back to the last page