Home Back

Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Fitaccen Dan TikTok, G Fresh Al'ameen, an Gano Dalili

legit.ng 2024/7/6
  • Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa hukumar Hisbah ta Kano ta kama fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al'ameen
  • An ce hukumar ta kama mawakin ne bayan tarin gargadi da ta yi masa kan kalamai, rawa da bidoyon batsa da ya ke yadawa
  • Haka zalika, ana zargin G-Fresh Al'ameen da yin izgili ga ayoyin Al-Kur'ani, wanda za a gurfanar da shi gaban kotu a gobe Litinin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al'ameen saboda zargin yi wa Al-Kur'ani izgili.

Babban daraktan Hisbah na jihar, Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar da kama G-Fresh ga manema labarai a ranar Lahadi.

Hisbah ta kama G-Fresh Al'ameen
Kano: Hisbah ta fadi dalilin kama G-Fresh Al'ameen. Hoto: Hisbah Board Kano, Gfresh Alameen Asali: Facebook

Shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito cewa hukumar ta kama fitaccen dan TikTok din ne bayan bijirewa gargadin da ta yi masa kan abubuwan da ya ke ɗora a intanet.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Sufi ya ce:

"Mun kama G-Fresh Al'ameen ne bayan tarin gargadi da muka yi masa kan abubuwan badala da ya je wallafawa a TikTok da sauran shafukan sadarwa."

Hukumar ta Hisbah ta ce za ta gurfar da G-Fresh a gaban kotu a gobe Litinin, 3 ga watan Yuni.

Wani rahoto da shafin rediyon Freedom na Kano ya fitar, ya nuna cewa Husbah ta kama G-Fresh saboda yin izgili ga ayoyin Al-Kur'ani.

Haka zalika, ana zargin fitaccen dan TikTok din, wanda kuma mawaki ne da furta kalamai da rawar batsa a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

People are also reading