Home Back

EFCC Ta Sanya Tukwici Ga Masu Fallasa Waɗanda Ke Wulaƙanta Naira

leadership.ng 2024/10/5
EFCC Ta Sanya Tukwici Ga Masu Fallasa  Waɗanda Ke Wulaƙanta Naira

A wani yunƙurin daƙile wulaƙanta Naira a wajen bukukuwa, hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta sanar da sanya tukwuicin kaso 5 cikin 100 ga duk wanda ya kawo mata labarin masu muzanta Naira har aka kai ga gurfanar da su.

Jami’in watsa labarai na EFCC, Dakta Dele Oyewale, shi ne ya shaida hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja cikin makon nan.Oyewale ya jaddada aniyar hukumar na tabbatar da doka da kare martabar tattalin arziki daga masu cin zarafin Naira.

Ya ce, kaso 5 na tukwuici an ware shi ne domin ƙarfafa gwiwar mutane da suke tona sirin masu cin zarafin Naira k6uma hakan zai taimaka wajen bayar da bayanai da za su kai ga cafkewa da gurfanar da masu cin zarafin Naira.

“Akwai tukwuici ga duk ani da ya kawo rahoton masu watsa Naira. Duk wanda ya tono asirin cin zarafin Naira zai samu kyautar kaso 5 cikin 100 na kuɗin da aka yi amfani da su wajen tafka ta’asar, amma muhimman bayanan da za su kai har a gurfanar da masu laifin ba wai bayanai na shaci faɗi ko ƙage ba,” Oyewale ya shelanta.

Ya ƙara da cewa EFCC ta gabatar da kusan mutum 50 a faɗin ƙasar nan tun lokacin da aka kafa sashin kar-ta kwana kan masu cin zarafin naira da dala.

Kakakin na EFCC ya kuma tabbatar da cewa ƙin amincewa da naira a matsayin wata doka babban laifi ne, kuma duk wanda aka kama da laifin hakan zai fuskanci hukunci mai tsauri. Ya ce, hukumar tana yin ƙoƙarinta wajen ganin ta samar wa Naira kima a idon sauran ƙasashen waje domin kyautata tattalin arziki.

Oyewale ya ce, “Laifi ne ƙin amsar naira, watakila ko don ya yi datti ko don ba sabbi ba ne, laifi ne hakan babba. “Naira ne alamin tattalin arzikinmu. Ƙasarmu tana dai Cikakken ƴancinta kuma dole harkokin cinikayyarmu su tafi da Naira a Nijeriya, don haka ƙin amincewa da Naira laifi ne.”

People are also reading