Home Back

Afirka ta Kudu: Tankiya a kan rabon mukaman gwamnati

dw.com 2024/7/6
Hoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Sai dai a cikin 'yan kwanakin nan, jaridun kasar, sun ba da rahoton samun tashin hankali a tattaunawar da ake yi tsakanin jam'iyyar  ANC da babbar jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance DA ta 'yan Liberal. A cewar wadannan bayyanai cikin kusan mukaman ministoci guda 30, Jamiyyar DA na bukatar samun goma yayin da ANC ta ce za ta iya ba su mukamai biyar ne kawai. A Afirka ta Kudun gaba daya jam'iyyun siyasa goma ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa musamman ANC. da  DA da wasu  kananan jam'iyyu  siyasa.

People are also reading