Home Back

An Yi Garkuwa Da Dalibai 1,680 Da Kashe 180 Cikin Shekara 10 A Nijeriya – UNICEF

leadership.ng 2024/5/18
An Yi Garkuwa Da Dalibai 1,680 Da Kashe 180 Cikin Shekara 10 A Nijeriya – UNICEF

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa an yi garkuwa da yara 1,680 yayin da kuma 180 daga cikinsu an kashe su ne tun lokacin da aka fara garkuwa da ‘yan makarantar mata a Nijeriya a shekarar 2014.

Wani sabon rahoton da asusun ya fitar na cewa kashi 37 ne kawai na makarantu daga jihohi 10 aka bayyana masu alamu masu tayar da hankali don su gane kamar kawo wa makaranta hari.

Hakan yana kasancewa ne yayin da Nijeriya cika shekara 10 tun lokacin da aka fara garkuwa da ‘yan makaranta masu yawa, inda ‘yan mata 91 a Arewa maso gabas har yanzu ana ci gaba da garkuwa da su,yayin da Nijeriya ke kara shiga wani alhini na ‘yan makarantar Kaduna wanda aka yi a watan Maris na wannan shekarar.

UNICEF ya yi kira da a daukai matakan da suka dace wajen kare kananan yara wadanda sune abin ya fi shafa.

“Dauka da garkuwa da ‘yan matan a makarantar Chibok wani jirwaye mai kamar wanka ne, mai nuna irin hadarin da yara ke shiga a kokarin da suke wajen neman Ilimi,”Ms Cristian Munduate wakiliyar UNICEF a Nijeriya ta ce lokacin da ake gabatar da rahoton a ofishin Majalisar Dinkin Duniya.

Ta ce a yau da ake tunawa da abin bakincikin na garkuwar da aka yi a sassa daban-daban na Nijeriya, “Hakan wata manuniya ce a kokarin da muke yi  domin kare lafiyar ‘ya’yanmu”.Wadannan alkalumma masu ta da hankali ba wai za mu tsaya kan alamu ba har ma abubuwan da suke sa ana samun su tashin hankalin da kan shiga.

“Ilimi wata dama ce da ake bi domin fita daga fatara, sai dai duk da hakan yawan kananan yara a Nijeriya har yanzu sun kasa cimma burinsu.

“Abin ya taso ne bayan wasu bayanai da aka samu na rahotanni masu ta da hankali na tashe- tashen hankula a makaranta da suka shafi garkuwa da dalibai lamarin da yake karuwa.

“Shekaru 10 da suka wuce an samu yin garkuwa da yara 1,680 lokacin da suke makaranta da wasu wurare, an kuma kashe 180 saboda harin da ake ka iwa makarantu, inda aka kiyasta an yi garkuwa da malamai 60 aka kashe 14, fiye da hari 70 da aka kai wa makarantu kamar yadda rahoton da aka tabbatar da sahihanci shi na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.”

Babbar jami’ar Ilimi, Saadhna Panday-Soobrayan ta bayyana haka ne a ofishin hukumar UNICEF lokacin da take bayar da rahoto a Nijeriya.

People are also reading