Home Back

Mutane miliyan 120 sun rasa muhallansu saboda yaƙe-yaƙe

rfi.fr 2024/7/1

Hukumar Kula da Ƴan cirani ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ƙaruwar mutanen da rikici ke tilastawa barin matsugunansu a sassan duniya, adadin da hukumar ke cewa zuwa yanzu ya kai mutum miliyan 120.

Wallafawa ranar: 13/06/2024 - 19:04

Minti 1

Kimanin mutane miliyan 120 sun rasa muhallansu saboda yaƙe-yaƙe a yankunansu.
Kimanin mutane miliyan 120 sun rasa muhallansu saboda yaƙe-yaƙe a yankunansu. © AFP - ISSOUF SANOGO

Alƙaluman da Hukumar Kula da Ƴan gudun Hijirar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar a yau Alhamis sun nuna cewa ƙaruwar rikice-rikicen da ake gani a wurare irin Gaza da Sudan da kuma Myanmar ya taka rawa wajen ƙara yawan mutanen da ake tilasta wa rabuwa da matsugunansu.

A cewar alƙaluman na UNHCR yanzu haka adadin mutanen da ke warwatse a wurare daban-daban sakamakon rikici, na matsayin daidai da adadin al’ummar Japan, batun da shugaban hukumar Filippo Grandi ke cewa rikice-rikicen da ƙasashe ke gani shi ne ummul'aba’isin ƙaruwar mutanen da ke rabuwa da muhallansu.

A cewar Grandi zuwa ƙarshen shekarar dubu 2023, mutum miliyan 117 da dubu 300 ne aka tilastawa rabuwa da muhallansu yayinda daga farkon shekarar nan zuwa ƙarshen watan Aprilu adadin kusan mutum miliyan 3 ya ƙaru da kaso mai yawa daga Gaza sakamakon hare-haren Isra’ila.

Hukumar ta UNHCR ta ce adadin mutanen da ke rasa matsugunansu a sassan duniya ya karu daga wanda aka gani a 2022 na mutum miliyan 110, kazalika a shekaru 12 kenan a jere ana ganin ƙaruwar adadin shekara bayan shekara tun daga shekarar 2012.

People are also reading