Home Back

Sanusi II Ya Yi Biris da Umarnin 'Yan Sanda, Ya Gudanar da Hawan Sallah

legit.ng 2024/7/6

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya gudanar da hawan Sallah domin bukukuwan babbar Sallah.

Sarkin na Kano ya jagoranci sallar idi inda ya yi huɗuba a masallacin Juma’a na kofar Mata.

Sanusi II ya yi hawan Sallah
Sanusi II ya yi hawan Sallah a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

An gudanar da Sallar Idi a masallacin Juma'a na Kofar Mata sakamakon ruwan sama da ya mamaye harabar filin Idi wanda hakan ya sanya ba za a iya amfani da shi ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran muƙarraban gwamnatinsa sun gudanar da sallar Idin tare da Sarkin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji, ƴan sanda da sibil difens da dai sauran su sun ba da tsaro.

Sarki Sanusi II ya bi hanyar da ya saba komawa gida, inda ya riƙa tsaya yana karɓar gaishe-gaishe daga wajen ɗaiɗaikun mutane sa ƙungiyoyi yayin da yake tafiya a kan doki.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da hana gudanar da hawan Sallah bayan wani taron tsaro na haɗin gwiwa da aka gudanar a jihar.

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin daɗinsa da matakin, inda ya nuna rashin jin dadin yadda ƴan sanda suka ɗauki wannan matakin ba tare da tuntuɓarsa ba a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar.

A halin da ake ciki, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi Sallar Idi a fadar Sarki da ke Nassarawa kamar yadda aka sanar tun farko.

Asali: Legit.ng

People are also reading