Home Back

InnalilLahi: An Shiga Ɗimuwa Bayan Ƙarin Rasuwar Mahajjatan Najeriya 2 Take a Makkah

legit.ng 2024/7/5
  • Mutane sun shiga tashin hankali bayan samun karin rasuwar mahajjata biyu daga jihar kwara da ke Arewacin Najeriya
  • Mahajjatan da aka bayyana da Salman Muhammad Alade da Ayishat Shuaib Ologele sun rasa ransu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Hukumar alhazan jihar Kwara ta tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da yi musu addu'ar samun rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - An samu rasuwar karin mahajjata guda biyu a kasar Saudiyya yayin aikin hajji.

Mahajjatan guda biyu sun fito ne daga jihar Kwara da aka bayyana da Salman Muhammad Alade da kuma Ayishat Shuaib Ologele.

Daily Trust ta tattoo cewa mutuwar mahajjatan guda biyu ya tabbatar da rasa akalla mutane hudu kenan daga jihar Kwara.

An tabbatar cewa Ayishat Shuaib Ologele ta rasa ranta ne yayin tafiya daga Makkah zuwa Madinah.

Yayin da Salman Muhammad Alade shi ma ya fadi rashin lafiyar a Makkah inda ya ce ga garinku nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto hukumomi ba su tabbatar da musabbabin mutuwar mahajjatan ba.Sai dai hukumar alhazan jihar Kwara ta jajantawa iyalan wadanda suka rasu inda ta yi addu'ar samun rahama a gare su.

Karin bayani ma tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading