Home Back

Yawan Marasa Aikin Yi A Nijeriya Ya Karu Da Kaso 5 A Karshen 2023 – NBS

leadership.ng 2024/4/29
Yawan Marasa Aikin Yi A Nijeriya Ya Karu Da Kaso 5 A Karshen 2023 – NBS

Yawan marasa ayyukan yi a Nijeriya ya karu a karshen zangon shekarar 2023 zuwa mataki na biyar cikin dari, a cewar hukumar kididdiga ta kasa (NBS).

 A wani rahoto da ta fitar kan ayyuka a karshen zangon 2023, wanda ta wallafa a ranar Litinin din nan da ta gabata, NBS ta ce, adadin ‘yan zaman kashe wando ya karu daga kaso 4.2 na tsakiyar zangon 2023 zuwa mataki 5.0 a karshen zangon shekarar 2023.

A cewar ofishin kididdigar, kusan kaso 4.1 na mutanen da ke da shekarun da ya dace a ce suna kan ayyuka ne, sun tsunduma harkokin da suka shafi noma, wani matakin aiki ne shi ma a wani barin.

Adadin shiga aiki ya ragu zuwa mataki 79.5 a karshen zangon 2023 daga kaso 80.4 na zango na biyu na shekarar 2023, hakan na nuni da raguwar masu samun guraben ayyuka.

 A cewar rahoton, yawan marasa ayyukan yi ya karu da kaso 17.3 a karshen shekarar 2023, sabanin kaso 15.5 na zango na biyu na shekarar 2023.

“Kusan kaso 87.3 na ma’aikata na aikin kashin kansu ne a karshen zangon 2023.

 “Adadin matsakaitan ayyuka ya kasance kaso 12.7 a karshen zangon 2023.

 “Adadin mutanen da ba su da ayyukan yi masu matakin karatun sakandari ya kai kaso 7.8 cikin 100 a karshen 2023.”

NBS ta kara da cewa yawan marasa ayyukan yi masu matakin shekara 15 zuwa 24 ya kai kaso 8.6 a karshen 2023, an samu karin kaso 1.4 idan aka kwatanta da na zango na biyu na shekarar 2023.

Rahoton ya ci gaba da cewa, “Yawan marasa aikin yi a yankunan karkara ya kai mataki 6.0 a zango na uku na 2023, inda aka samu kari a kan na zango na biyu da kaso 0.1.”

 
People are also reading