Home Back

'Ana sayar wa Larabawa ƴan-ciranin Nijar a kurkukun Libya kamar bayi'

bbc.com 2024/8/22

Asalin hoton, AP

.
Bayanan hoto, Daruruwan 'yan ciranin Afirka ne ke mutuwa a kokarin tsallaka tekun Bahar Rum dan isa Turai

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai bakin haure kusan 160,000 da suka fito daga jamhuriyar Nijar a yanzu suke kasar Libya.

Kuma kusan kashi 25 cikin 100 na bakin hauren da ke zaune a daukacin kasar, kashi mafi girma na 'yan ciranin da suka fito ne daga kasashe daban-daban.

Sai dai halin da 'yan Nijar din da ke kasar Libya musamman wadanda ba su da ko takardar tsire ta shaidar zama kasar Libya, na cikin mawuyacin hali, yawanci sun kare a gidajen kaso.

Sun yi kira ga hukumomin Nijar su taimaka su maida su gida sakamakon mummunan halin da suke ciki a can.

Wani dan Nijar da bai yarda a ambaci sunanshi ba, da kuma yake zaman boyo a Libya ya shaida wa BBC cewa halin ukubar da suke ciki ya munana.

''Wallahi halin da ake ciki ya munana a gidajen kaso, ko mutuwa ka yi ka mutu kare ya fi ka daraja, idan kana tafe ba ka da daraja, haka a wurin aiki, haka kuma a gidan kaso, idan an kai ka kurkuku Allah Ya taimaka kana da dan kudi sai ka biya a fidda ka, amma fa kwana biyu idan an sake kama ka nan za a maido ka,'' In ji shi

Ya kara da cewa : ''Talauci ne ya fiddo mu daga gida, nan da muka zo babu kwanciyar hankali, can gida babu abin yi.''

Mutumin ya ce, ƴan Libya ba sa barinsu da komai, kama daga kaya ko kudi, kai hatta mutum kanshi bai tsira ba sai guje-guje da wasan buya da 'yan kasa, a kama ka a kuma kai ka kurkuku.

''A cikin kurkuku ba ka tsira ba domin saida wa wani Balarabe kai za a yi, ya tafi da kai ka yi masa aiki da zarar aikin ya kare ya sake dawo da kai inda ya dauke ka, '' in ji shi.

''Kashi 80 cikin 100 na 'yan Nijar da ke nan Libya na son komawa gida, amma ba mu da kudin mota idan ma kana da shi da ka fita hanya za a tare ka a kwace, idan ka fita daga birnin Tripoli kafin ka kai Sabha sun kwace komai a hannun ka.'' Acewarsa.

A karshe ya yi kira ga shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya taimaka musu, ya kuma ce;

''Mu fa 'yan Nijar muna shan wahala mun kawo kuka gare ka, ka tashi ka tsaya ka gani. Jakadan Libya yana Yamai, jakadanmu yana nan Libya amma abin ya fi karfinshi ba zai iya shi daya ba. 'yan Libya na zaune a Nijar birjik cikin walwala da kwanciyar hankali, babu mai yi musu magana. Idan abin ya ki yiwuwa a maido mu gida, a aiko motoci cikin watanni 6 duka 'yan Nijar da ke Libya za su dawo gida.''

Libya dai ta kasance hanyar da dubban bakin haure da ke son shiga Turai ta teku a duk shekara suke jibge, inda galibi ke fadawa hannun kungiyoyin masu fataucin mutane da ke karbar kudi.

People are also reading