Home Back

Nuhu Ribadu Ya Kawo Muhimman Dalilai 2 da Suka Haddasa Rashin Tsaro a Najeriya

legit.ng 2024/5/3
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya yi magana kan matsalar rashin tsaronda ake fama da ita a ƙasar nan
  • Nuhu Ribadu ya bayyana cewa yawaitar ƙanaanan makamai da cin hanci da tsaro su ne manyan dalilan da suka haddasa rashin tsaro a ƙasar nan
  • Ya yi nuni da gwamnati mai ci ta Shugaba Bola.Ahmed Tinubu ta samu nasarori a fannin samar da tsaro tun bayan kafuwarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana dalilan da ke ƙara kawo matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Nuhu Ribadu ya bayyana cewa yawaitar shigo da ƙananan makamai, cin hanci da rashawa da kuma rashin adalci ne suka haddasa rashin tsaro a ƙasar nan.

Nuhu Ribadu ya magantu kan rashin tsaro
Nuhu Ribadu ya yi magana kan rashin tsaro a Najeriya Hoto: Nuhu Ribadu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakan a jami’ar Usman DanFodio da ke Sakkwato a lokacin da yake gabatar da wata lacca.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ribadu ya bayyana cewa duk da cewa akwai dokar hana mallakar makamai ba tare da izini ba, ana ta yawo da ƙananan makamai wanda hakan ke haddasa tashin hankali, cewar rahoton jaridar Blueprint.

Ribadu ya fadi matakan da ake ɗauka

Ya ce gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki matakai da dama domin rage yawaitar ƙananan makamai wanda a cewarsa ya samar da sakamako mai kyau, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a fannin tsaro a ƙarƙashin gwamnati mai ci ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya nanata cewa an samu nasarar cewa ceto wasu ƴan makaranta da aka sace ba tare da biyan ko sisi ba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta inganta tsaro a yankin Neja Delta wanda hakan ya taimaka wajen haɓaka haƙo mai a yankin.

An buƙaci Tinubu ya kori Nuhu Ribadu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an ba shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara da ya tsige babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro kuma tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Nuhu Ribadu.

Wani marubuci mazaunin Abuja, Abbah Modibbo, ya yi wannan kiran inda ya bayyana cewa Ribadu bai cancanci rike wannan muhimmin muƙamin ba

Asali: Legit.ng

People are also reading