Home Back

Me ya sa Boko Haram ke amfani da mata wajen harin ƙunar-baƙin-wake?

bbc.com 4 days ago
...

Asalin hoton, Getty Images

Wasu hare-haren ƙunar baƙin wake biyu da aka kai jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya a kwanakin baya-bayan nan ya ƙara jefa shakku da kuma ɗar-ɗar a zukatan jama'a kan iƙirarin da gwamnati take yi na murƙushe ayyukan masu tayar da ƙayar baya a ƙasar.

A ranar Asabar ne hare-haren biyu da ake zargin mata ƴan ƙunar baƙin wake da kaiwa suka yi ajalin aƙalla mutum 18 a garin Gwoza - ɗaya daga cikin manyan garuruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da a baya ake gani a matsayin cibiyar Boko Haram.

Wannan ne karo na uku cikin wata huɗu da Boko Haram ke kai munanan hare-hare ta hanyar amfani da abubuwan fashewa da suka jikkata tare da halaka mutane a jihar Borno.

Hare-haren na baya-bayan nan ya sa mutane na tunanin ko watakila ƙungiyoyin da ke ikirarin Jihadi na son farfadowa tare da gwada karfinsu.

Kunar bakin waken da matan suka kai ya sa mutane neman sanin ko me ya sa Boko Haram ke yawan amfani da mata wajen kai hare-haren ƙunar baƙin wake?

BBC ta yi nazari kan salon hare-haren na Boko Haram a baya, ta kuma tuntubi masana da suka yi nazari tare da ƙarin haske kan lamarin.

Harin kungiyar Boko Haram da ya dauki hankalin duniya shi ne a Afrilun 2014 inda mayakan suka kitsa sace ƴanmata 276 daga wata makaranta a Chibok - garin da ba shi da nisa sosai daga Gwoza. Fiye da ƴanmatan 100 har yanzu ba a ji ɗuriyarsu ba.

Bayan sace yan matan ne kuma, kungiyar ta kai wani hari a watan Yuni, inda ta yi amfani da mace da ta kai wani harin kunar bakin wake, shekara uku ke nan bayan da kungiyar ta kai harin kunar bakin wake karon farko.

Tun lokacin kuma, an yi ta samun rade-radin cewa matan da Boko Haram ke amfani da su wajen harin kunar bakin wake watakila su ne ƴanmatan Chibok da aka sace.

Salon yin amfani da mata wajen kai harin ƙunar baƙin wake tun lokacin ya ƙaru inda masana fannin tsaro ke danganta hakan ga ƙaruwar rikicin Boko Haram.

Rahotanni sun ce kungiyar ta fi amfani da mata a matsayin masu ƙunar baƙin wake fiye da duk wata kungiyar tayar da kayar baya a tarihi.

Babu dai wani tartibin bayani kan abin da ya sa Boko Haram ke amfani da mata mata wajen aiwatar da muggan ayyukanta da kai hare-haren ƙunar bakin wake sai dai ana ganin yanayin shigarsu ta hijabi daga sama har kasa na samar da hanya maio sauƙi wajen ɓoye bama-baman.

Mata sun kasance masu rauni sannan ba a cika nuna ayar tambaya a kansu ba, a don haka ba a zurfafa bincike a kansu idan aka kwatanta da maza.

Ƙididdigar da aka yi a baya-bayan nan ta nuna mata ne suka kai fiye da rabin hare-haren ƙunar bakin wake da Boko Haram ta kitsa.

People are also reading