Home Back

An Kiyaye Yin Kwaskwarima Kan Tsarin Jam’iyyar Kwaminis Ta Sin Da Kanta

leadership.ng 6 days ago
An Kiyaye Yin Kwaskwarima Kan Tsarin Jam’iyyar Kwaminis Ta Sin Da Kanta

Ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2024, rana ce ta cika shekaru 103 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta Sin. Tun lokacin da jam’iyyar ta kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, jam’iyyar ta kiyaye mulkin kasar cikin shekaru 75, wadda ta kasance jam’iyyar da ta fi tsawon lokaci kan mulkin kasa a tarihin duniya na wannan zamani.

Babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin raya jam’iyyar a sabon zamani wato yin kwaskwarima kan tsarin jam’iyyar da kanta, kana ya mai da ra’ayin a matsayin hanyar cimma burin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa da magance juyin mulki a kasar. A ganinsa, tilas ne jam’iyyar ta tuna da fasahohin mulkin kasa, da bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, da bunkasa tattalin arzikin kasuwa, da daidaita kalubale daga kasashen waje, da ganin kasancewar yanayin gajiyar yin kokari, da hana rashin karfi da kasa yin la’akari da jama’a, da kuma yaki da cin hanci da rashawa a kasar. Ya kamata a sa kaimi ga kiyaye yin kwaskwarima kan tsarin jam’iyyar da kanta. Tun daga lokacin da Xi ya zama babban sakataren, ya kiyaye kyautata tsarin yin kwaskwarima, da sa kaimi ga raya jam’iyyar bisa tsattsauran matakai a dukkan fannoni, da tabbatar da dabi’a mai kyau da yaki da cin hanci ko da yaushe, da jagorantar jam’iyyar da jama’ar kasar Sin wajen raya sha’anin kasar bisa tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin. (Zainab Zhang)

People are also reading