Home Back

Abubuwa Tara Game Da Babban Limamin Kasar Ghana, Sheikh Sharubutu Mai Shekaru 104 A Duniya

leadership.ng 2024/6/2
Sharubutu

Yana da shekaru 104, babban limamin kasar Ghana, Sheikh Usman Nuhu Sharubutu har yanzu yana da karfi da kuzari da cikakkiyar lafiya.

Sharubutu ya yi fice wurin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai na addini, ya tanadar da ka’idodi da ayyuka na gari ga duk wanda zai maye gurbinsa.

Sheikh Usman Nuhu Sharubutu, shi ne babban limamin Ghana na farko na kasa, wanda ya ke rike da mukamin tun shekaru talatin da suka gabata. Ba wai a kasa kadai ake girmama shi a matsayinsa na hazikin malamin addinin Musulunci ba, ya samu kyaututtuka a matsayinsa na jagora mai wanzar da zaman lafiya, mai fafutukar tabbatar da juriya da hakuri a addini da hadin kan kasa.

Sheikh Sharubutu dan darikar Tijjaniyya ne, amma yana mutunta duk wadanda suke da sabanin akida, don haka ya zama mai wakiltar muradun daukacin Musulmin kasar, su miliyan 6.1.

A yanzu dai, akwai babban kalubale ga Shehin Malamin kan yadda za a maye gurbinsa, kuma hakan shi ne batu mai mahimmanci a tsakanin musulmin Ghana.

Ga abubuwa tara da ya kamata ku sani game da Sheikh Sharubutu:

An haifi Sheikh Sharubutu a ranar 23 ga Afrilu, 1919 a tsohuwar Fadama a cikin babban yankin Accra, da ne ga Sheikh Nuhu Sharubutu da mahaifiyarsa, Hajiya A’ishatu Abbass, ya fito ne daga dangin da suka yi fice wajen koyarwa da tarbiyyar addinin Musulunci. Ya fara karatun Islamiyya a gida, iyayensa ne suka koyar da shi.

1. Rayuwarsa ta farko

Yana da shekaru 12, ya yi fice a cikin matasa da iya karatun Alkur’ani a Ghana. Saboda irin wannan baiwa da Ubangiji ya kebe shi da ita, sai aka tura shi birnin Kumasi da ke yankin Ashanti na kasar Ghana, domin yin karatu a gaban wasu fitattun malaman addinin Musulunci, bayan kammala karatunsa, sai ya dawo Accra ya fara aikin koyarwa na addinin Musulunci.

A shekara ta 1974, ya shahara a matsayin malami a cikin al’ummar musulmi.

2. Taso wa zuwa ga daukakarsa

A shekarar 1974, shugabannin darikar Tijjaniyya suka zabe shi a matsayin mataimakin babban mukaddamin ‘yan darikar Tijjaniyya a Ghana. Da farko yaki amincewa amma daga baya ya amsa umurnin. A shekarar 1993 ya zama babban mukaddamin darikar Tijjaniyya a kasar bayan da dan uwansa da ke rike da mukamin ya yi murabus saboda rashin lafiya.

A shekarar 1992, karkashin shugaba Jerry John Rawlings, gwamnati ta goyi bayan kafa ofishin babban limamin kasar Ghana a hukumance wanda zai rika magana da yawun musulmi a kasar.

Gwamnatin ta kuma kafa wani kwamiti da ya kunshi wakilai daga dukkan kungiyoyin Musulmai – darikar Tijjaniyya, Izala, Ahmadi da Shi’a – don zabar shugaba daya. Kwamitin ya zabi Sheikh Usman Sharubutu a matsayin wanda zai fara zama shugaban ofishin.

3. Jakadan zaman lafiya

Sheikh Sharubutu, ya yi fice a tarihin Ghana don hakuri da juriyar addini da hadin kan kasa, inda ya yi kokarin tabbatar da zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmi a kasar.

Baya ga lambar yabo daga masu ruwa da tsaki daban-daban, Majalisar dinkin Duniya a Ghana ta karrama shi a watan Yulin da ya gabata. A cikin 2016, ya sami lambar yabo ta Martin Luther King karo na tara don tabbatar da zaman lafiya da adalci daga ofishin jakadancin Amurka a Ghana. Jami’ar Ghana ta kuma ba shi lambar yabo ta ‘DAKTA’ na girmamawa saboda rawar da ya taka wajen sasanta rikice-rikice daban-daban a kasar da kuma tabbatar da hadin kan kasa.

4. Jajircewarsa ga ilimi

A bisa shaidar da ya samu na son ilimi, ya kafa Asusun Tallafawa Ilimi mai suna ‘Sheikh Usman Nuhu Sharubutu trust fund’ wanda ya baiwa dalibai fiye da 4,000 lamuni. Haka kuma, Asusun yana daukar nauyin karatun yaran musulmi, yana ginawa, gyarawa da kula da makarantu a fadin kasar Ghana.

5. Tsarinsa na tarbar baki

Baya ga ziyarar da manyan baki da jami’an gwamnati da na kamfanoni da sauran masu fada a ji da suka saba yi, babban limamin kasar na bude kofarsa ga daidaikun mutane daga kowane bangare na duniya. Tun daga yaran da suke ziyartar gidansa don karin kumallo da abincin dare, da matasa masu ziyartarsa don yi musu addu’a, yana kuma amsa kiran taron al’umma a duk inda suke.

Hakan ya sa wasu daga cikin al’ummar Musulmi suka koka kan adadin mutanen da ake bari su na gana wa da shi, bisa la’akari da lafiyarsa da darajar ofishinsa.

Har yanzu yana halartar taron kasa da sauran tarukan da daidaikun musulmi suka shirya. Bayanai daga ofishinsa sun ce, ya zuwa yanzu ya gudanar da auren musulmi fiye da 5,000, ya jagoranci sallar jana’iza ta musulmi  fiye da 4,000 da kuma bukukuwan radin sunayen jarirai fiye da 10,000.

6. Tarihinsa kan ziyartar Coci

Sheikh Sharubutu ya samu yabo daga mutane da dama a shekarar 2019 lokacin da ya zauna a layin farko na Cocin Katolika da ke Accra wacce ke karkashin kulawar ‘Christ the King Catholic’ a lokacin bikin Ista.

Yayin da mutane da yawa ke yaba wa matakin a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa, akwai masu suka da suke ganin hakance ya sabawa addinin Musulunci.

“Ban je wurin yin ibada ba. Ziyara ce ta abokantaka,” in ji Sheikh Sharubutu a wata hira da ya yi da tashar Tb3 ta Accra ta bakin wani mai fassara.

A watan Satumba, ya ziyarci babban ofishin Cocin Yesu Almasihu na kasa da ke kasar.

7. Shirin wanda zai maye gurbinsa

A lokacin da aka kafa ofishin babban limamin kasa, an amince da cewa, za a rika juya matsayin a tsakanin kungiyoyin daban-daban. Amma dai, duk da haka, shirin wanda zai gaji kujerar, lamari ne wanda ke cike da rudani.

A shekarar 2019, aminin Sheikh Usman Sharubutu kuma mataimakin babban limamin kasa, Sheikh Ahmad Kamaludeen, ya rasu yana da shekaru 103.

A shekarar da ta gabata, ministan harkokin addini, Stephen Asamoah Boateng, ya sake jaddada bukatar fayyace tsarin maye gurbin kujerar babban limamin kasa a fili.
Duk da cewa, wasu daga cikin kungiyoyin Musulunci da ke kasar, na fargabar katsalandan din ‘yan siyasa wajen maye gurbin babban limamin kasa na gaba.
Amma dai, Babban Lauyan Gwamnati Godfred Dame ya ce, gwamnati “ba ta da hannu ko sha’awar wanda zai zama shugaban darikar Katolika, Methodist ko Presbyterian Mission a Ghana”.

8. Sanarwar hutun bukukuwan Sallar Eid

Babban limamin kasa ya taka rawar gani wajen ganin gwamnatin Rawlings ta ba wa musulmi hutun bukukuwan Eid-el-Fitr da Eid-ul-Adha a shekarar 1995.

Wadannan bukukuwan, sun kasance a cikin Dokar Hutu na Jama’a na yanzu da aka yi wa kwaskwarima (2019), (Doka 986).

9. Iyalinsa

Babban Limamin na kasa, ya yi kokarin hana iyalinsa shiga cikin harkokin ofishinsa saboda wasu dalilai da ba za a iya bayyanasu a bainar jama’a ba.

Yana auren Hajiya Adiza Usman da Hajiya Ramatu Nuhu Sharubutu. Wasu ‘ya’yansa maza suna aiki tare da shi.

People are also reading