Home Back

Mene Ne Bambancin Ra’ayi Na Kasar Sin Dangane Da Tsarin Kasa Da Kasa ?

leadership.ng 3 days ago
Mene Ne Bambancin Ra’ayi Na Kasar Sin Dangane Da Tsarin Kasa Da Kasa ?

Yayin ziyarar Yusuf Maitama Tuggar, ministan harkokin wajen kasar Najeriya, a kasar Sin a kwanan baya, wata maganar da ya fada ya burge ni, inda ya ce, “Yadda kasar Sin ke kallon tsarin kasa da kasa ya sha bamban da na sauran kasashe: Ba ta kallon duniya a matsayin filin dambarwar siyasa, maimakon haka, tana neman karfafa hadewar yankuna da kasashe, ta shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.”

Wannan bambanci game da kasar Sin da minista Tuggar ya ambata ya samu tabbatuwa ta bakin mutanen sauran kasashe. Misali, Roger McKenzie, wani editan jaridar Morning Star ta kasar Birtaniya, ya fada a cikin wata makalar da ya rubuta da cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kasar Sin ta gabatar na neman karfafa mu’ammalar abokan hulda a fannin manufofi, da hade kayayyakin more rayuwa, da ingiza ciniki, da dunkulewar tsarin kudi, gami da tabbatar da fahimtar juna tsakanin mabambantan al’ummu. Wanda a cewarsa, ya sha bamban da ra’ayin kasar Amurka na “Ba ni goyon baya, in ba haka ba, ka zama abokin gaba. ”

To, idan mun tantance dalilin da ya sa kasar Sin ke samun bambancin ra’ayi, za mu fahimci cewa, hakan na kasantuwa ne bisa ra’ayin kasar na “gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya”. Wato a ganin kasar Sin, tsakanin mabambantan kasashe akwai matsayi na daidaituwa. Kana duk wadannan kasashe suna da makomar bai daya. Saboda haka, ya kamata su zama tare cikin zaman lafiya, da more hakki na bai daya, da kokarin hadin gwiwa wajen tinkarar kalubaloli, don tabbatar da cikakkiyar walwalar dukkansu. Sa’an nan idan an yi karin nazari kan ra’ayin na kasar Sin, za a gano asalinsa shi ne daga ka’idoji guda 5 na tabbatar da zama tare cikin lumana, da kasar Sin ta gabatar wasu shekaru 70 da suka wuce, wato girmama wa juna ikon mulkin kai da cikakken yankin kasa, da magance kai hari ga juna, da rashin tsoma baki cikin harkokin gida na juna, da kokarin amfanawa juna cikin daidaito, gami da zama tare cikin lumana. Inda ka’idojin 5 sun nuna yadda kasashe masu tasowa suka yi kokarin kare moriyar kai daga wasu kasashen da ke neman yin babakere a duniya, gami da al’adun gargajiya na kasar Sin na kula da sauran mutane kamar yadda aka kula da kai, da kokarin nuna kauna ga makwabta.

A bisa ra’ayi na “gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”, ya kamata a yi kokarin tabbatar da daidaituwa da cin moriya tare, a tsakanin kasashe daban daban, yayin da suke hadin gwiwa da juna. To, dangane da haka, an samu dimbin shaidu cikin hadin gwiwar Sin da Afirka: Zuwa yanzu, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kokarin ginawa kasashen Afirka layin dogo na tsawon kilomita 6000, da hanyoyin motoci na kilomita 6000, da tashoshin jiragen ruwa da yawansu ya kai kusan 20, da manyan tashoshin samar da wutar lantarki fiye da 80. Haka zalika, kasar ta zuba jari da gina yankunan masana’antu 25 a kasashen Afirka, inda aka dauki ma’aikata ‘yan Afirka dubu 42, da taimakawa kokarin kasashen Afirka na raya bangaren masana’antu, da sauya tsarin tattalin arzikinsu. Ban da haka, na taba gamuwa da dimbin dalibai ‘yan Afirka da suka zo kasar Sin karatu, da ‘yan kasuwa masu yin cinikayya tsakanin bangarorin Sin da Afirka, da kwararru masu fasahar aikin gona na kasar Sin da suke kokarin yada fasahohin noma na zamani a kasashen Afirka, da Sinawa masu zuba jari da masu kamfanoni da suka dade suke zama a nahiyar Afirka, da dai sauransu. Wadannan mutane na kokarin neman cika burikansu, ta hanyar halarta cikin cudanya da hadin gwiwar Sin da Afirka, da ingiza cudanya tsakanin mabambantan al’ummu da al’adu, tare da samar da gudunmowa ga yunkurin kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya.

Hakika, a nawa fahimta, abin da minista Tuggar ke nufi shi ne, ra’ayin kasar Sin kan tsarin kasa da kasa ya sha bamban da na wasu kasashen dake yammacin duniya, wadanda ke neman kare yanayinsu na babakere a duniya. Amma idan an kwatanta da ra’ayoyin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka, da na kasar Sin, to, za a ga suna da ra’ayi daya. Inda suke neman magance son kai, da ja-in-ja, da tsarin kashin dankali, gami da rungumar ra’ayin zama tare cikin lumana, da hadin gwiwa da amfanin juna, da kuma neman samun ci gaba na bai daya. To, wannan ra’ayi nasu ya nuna hanya mai dacewa da ya kamata a bi, don neman tabbatar da ci gaban duniya, da na harkokin daukacin dan Adam. (Bello Wang)

People are also reading