Home Back

NNPC Ta Sanya Dokar Ta Ɓaci A Fannin Haƙo Mai

leadership.ng 2 days ago
NNPC Ta Sanya Dokar Ta Ɓaci A Fannin Haƙo Mai

Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya kafa dokar ta-baci kan haƙo mai da iskar gas a Nijeriya, tare da yin kira da a haɗa kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin tunkarar kalubalen a fannin. 

A yayin taron baje kolin mai da iskar gas na Nijeriya karo na 23 da aka yi a Abuja, babban jami’in gudanarwa na ƙungiyar Engr. Mele Kyari ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai domin shawo kan matsalolin da ke hana hako danyen mai yadda ya kamata.

Kyari ya yi nuni da cewa, idan aka kula da kuma ɗaukar matakan da ya dace, Nijeriya za ta iya haƙo ganga miliyan biyu na ɗanyen mai a kowace rana idan aka zuba jari da sabbin na’urori, amma rashin inganci da tsaikon sayo wa ke kawo cikas ga ci gaba.

Kyari ya bayyana cewa, hukumar ta NNPC da abokan hulɗarta za su magance waɗannan ƙalubale ta hanyar ɗaukar matakai kamar maye gurbin tsohon bututun ɗanyen mai da kuma aiwatar da shirin raba rigima domin kula da na’urorin da ake haƙowa a ƙasar nan na tsawon shekaru huɗu zuwa biyar.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da masana’antu da su yi aiki tare don rage farashin samarwa da haɓaka kayan aiki zuwa matakan da aka ƙuduri niyya. Bugu da kari, Kyari ya bayyana ƙudirin NNPCL na saka hannun jari a muhimman kayan aiki na iskar gas, kamar su Obiafu-Obrikom-Oben (OB3) da bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK), don bunƙasa samar da iskar gas a cikin gida da samar da wutar lantarki da ci gaban masana’antu.

People are also reading