Majalisa Za Ta Binciki Kwangilar Aikin Mambila, Za a Dauko Aikin Wutar Tun Daga 1999
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta dauki sabon mataki kan aikin wutar Mambila da aka warewa makudan kudi.
A lokacin mulkin Muhammadu Buhari aka yi tsammanin fara amfanuwa da wutar amma sai aikin ya gagara samuwa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar ta tattauna kan lamarin ne a zamanta na jiya Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta umurci kwamiti mai lura da harkar makamashi da kudi ya fara bincike kan yadda aka kashe kudi a aikin wutar Mambila ba tare da samar da lantarki ba.
Rahoto ya nuna cewa binciken majalisar zai fara ne tun daga shekarar 1999 har zuwa lokacin mulkin Muhammadu Buhari.
Sanata Manu Haruna daga Taraba ta tsakiya ne ya jawo hankalin majalisar kan aikin wutar, rahoton Business Day.
Daga baya kudurin ya samu goyon bayan Sanata Danjuma Goje, Ahmed Lawan da wasu Sanatoci su 26.
Sanata Danjuma Goje ya ce zai ba da dukkan goyon bayan da ake buƙata domin tabbatar da cewa an yi aikin wutar Mambila.
Goje ya yi kira ga Bola Tinubu kan saka aikin wutar Mambila cikin manyan ayyukan da gwamnatinsa za ta yi.
Tun a shekarar 2017 gwamantin Najeriya ta ba kamfanin kasar Sin kwangilar aikin a kan $5.92bn amma aikin ba yiwu ba har yau.
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Muhammadu Inuwa Yahaya ta dauki mataki kan kansila da dagaci bisa zargin sata.
Ana zargin kansilan da dagacin da hada baki wajen sace randar wutar lantarki a Garin Majidadi da ke ƙaramar hukumar Akko.
Asali: Legit.ng