Home Back

An Kunyata Tinubu a Faifan Bidiyo Yayin Taro A South Africa? an Fayyace Gaskiyar Lamarin

legit.ng 2024/7/2

Fadar shugaban kasar Najeriya, ta ƙaryata bidiyon da ake yadawa kan kunyata Bola Tinubu a kasar Source Africa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

South Africa - Fadar shugaban kasa ta ƙaryata labarin da ake yadawa cewa an kunyata Bola Tinubu a kasar South Africa.

An yi ta yaɗa labarin cewa shugaban kasar, Cyril Ramaphosa ya ki gaisawa da Tinubu yayin bikin rantsar da shi.

Yar fafutuka, Aisha Yesufu ta wallafa wani faifan bidiyo a shafin X inda ta ce an kunyata Tinubu yayin da Ramaphosa yaki gaisawa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai daga bisani, TVC News ta wallafa wani faifan bidiyo inda aka gano suna gaisawa da Tinubu.

Har ila yau, hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, O’tega Ogra ya ce mai gidansa na layi na biyu inda aka ware sahun farko saboda masu sarauta na South Africa.

Ogra ya ce Ramaphosa ya fara gaisawa da wadanda ke gaba aka kira shi ya zauna saboda lokacin gaisuwar bai yi ba.

Ya ce daga bisani Ramaphosa ya zagaya har inda su Tinubu ke zaune a sahu na biyu inda suka gaisa cikin mutunta juna.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading