Home Back

Hana shiga sahun masu aikin Hajji

bbc.com 2024/7/3
.
.
Bayanan hoto, Maniyyata aikin Hajji a cikin masallacin Harami dake Makka

Saad al-Qurashi shi ne mai ba da shawara a hukumar Hajji da Umra wanda ke kula da kamfanoni masu zaman kansu na ƙasashen waje.

Ya shaida wa BBC cewa mutane da dama irin Sulaiman na gane cewa sun faɗa hannun 'yan damfara bayan sun isa ofishinsu.

Asalin hoton, Saad al-Qurashi

Saad al-Qurashi
Bayanan hoto, Saad al-Qurashi

Mutanen na samun mummunan labari ne a lokacin da suka yi yunƙurin karɓar takardar da maniyyata ke sanyawa a hannunsu da ke nuna cewa maniyyata ne da suka je Saudiyya bisa ƙa'ida.

“Lokacin da mutanen suka zo mana da takardar izinin aikin Hajji ta bogi, sai muka gano cewa sun karɓi jabun takardu da katunan shaida daga kamfanonin bogi, idan hakan ta faru sai a hana mutum zuwa aikin Hajji, sannan ya yi asarar kuɗi mai yawa."

Al-Qurashi, wanda ke aiki a kwamitin da ke Majalisar Dokokin Saudiyya, ya yi nuni da cewa, gungun ƙungiyoyi da dama sun yi ta kai hare-hare musamman a ƙasashen Masar, Siriya da Iraƙi a wannan lokacin na Hajjin.

Ya ce a sati yana ganin aƙalla mutum uku da aka cuta, wanda yawancinsu daga Masar ko Siriya da Iraqi suka taho.

.

Asalin hoton, Getty Images

Gargaɗi kan neman izinin Hajji a ƙurarren lokaci

Al-Qurashi ya yi gargadin cewa a kula da kamfanonin da ke ba da "izninin aikin Hajji a ƙurarren lokaci," waɗanda galibinsu ke ba da farashi mai sauƙi wanda hankali ba zai iya ɗauka ba, kuma suna tallatawa ne a shafukan sada zumunta.

Suleiman al-Shaer, wanda ya zanta da BBC ta wayar tarho a lokacin da yake zaune a ofishin hukumar Hajji da Umrah ta Saudiya, ya ce ya yi kuskure ta hanyar tura kuɗaɗe ga wani kamfani da ya kwashe lokaci kaɗan yana tantancewa.

Ya kuma shawarci mutane su guji aika kuɗi ga ɗaiɗaikun mutane ko wakilan kamfanonin ƙetare, da za su iya amfani da hanyoyin da ba na hukuma ba wajen ba da izinin Hajji.

Shaidar ƙarya kan tallace-tallacen shafukan sada zumunta

Ba Sulaiman kaɗai ne kawai irin wannan lamari ta shafa, akwai Farouk Abdel Wahab, wani likita mazaunin Birtaniya.

Ya shaida wa BBC cewa bai taɓa tsammanin shi da iyalansa za su samu kansu cikin yanayin da suka tsinci kansu bayan biyan kuɗin izinin aikin Hajji ga wani kamfanin yawon buɗe ido na Birtaniya.

Asalin hoton, Farouk Abdel Wahab

Farouk Abdel Wahab
Bayanan hoto, Farouk Abdel Wahab

Farouk, wanda ɗan asalin Pakistan ne ya shaida wa BBC cewa ya yi faɗa sosai tsakaninsa da kamfanin da ya yi masa alƙawarin abin da ba zai samu ba.

Ya samu sun mayar masa da fam dubu 7,000 da suka biya kamfaninsa da ƴan uwansa shekaru uku da suka gabata, inda ya samu nasarar zuwa aikin Hajji shekaru uku bayan damfararsa.

Al-Haram

Asalin hoton, EPA

Faruk ya ce gaf da ɓarkewar cutar korona, ƴan uwansa shida da shi sun yi niyyar yin aikin hajji. "Sai muka nemi kamfani mai zaman kansa muka biya su kuɗin kujerun hajji.

"Amma sai aka soke aikin Hajji a shekarar saboda korona. Sai muka nemi su mayar mana da kuɗinmu, amma ba su ce mana komai ba har tsawon shekara guda, hakan ya sa na kai su ƙara kotu, kuma kotun ta ba da umarnin su biya mu kuɗinmu.

Faruk ya ce a lokacin da yake tattara bayanan kamfanin domin shigar da ƙara ne ya gane an dakatar da kamfanin daga aiki.

Asalin hoton, Farouk Abdel Wahab

.
Bayanan hoto, Farouk Abdel Wahab ya ɗauki hoton allon sanarwar da ke gargaɗi kan masu zuwa aikin Hajji ba tare da izini ba

'Amana ce, ɗan'uwa'

Ya ce a lokacin da ya yi ƙoƙarin dawo da kuɗaɗen, wakilan kamfanin sun yi amfani da "kalaman addini."

Sun riƙa cewa wannan "amana ce, ɗan'uwa" kuma mun himmatu wajen mayar maka da kuɗin ka."

"Sai da bidiyona ya bazu kamfanin ya fara tuntuɓata tare da mayar mini da kuɗin ta wani kamfani," in ji shi.

BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar kamfanin, sai dai ba su amsa saƙonnin da aka aika musu ta adireshinsu na intenet da saƙonnin waya a lambar da suka sanya a shafukansu na sada zumunta.

Asalin hoton, Farouk Abdel Wahab

Farouk Abdel Wahab
Bayanan hoto, Hoton Farouk a lokacin da ya gabatar da Umra gabanin aikin Hajji

Hanyoyin kariya

Ƴan sandar Birtaniya sun shawarci al'umma su kula wajen zaɓen kamfanin da za su yi hulɗa da su waɗanda aka amince da su kamar ƙungiyar kamfanonin shirya tafiye-tafiye ta Birtaniya.

Yawanci ƙasashe na da irin waɗannan ƙungiyoyi, kamar Ƙungiyar Kamfanonin shirya tafiye-tafiye ta Najeriya da kuma ƙungiyar masu shirya tafiye-tafiye ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Ƙungiyar kamfanonin shirya tafiye-tafiye ta Birtaniya ta shawarci masu tafiye-tafiye da su tabbatar sun ajiye dukkan takardun yarjejeniyar da aka sanya hannu, mai ɗauke da ƙa'idoji, su daina amincewa da magana ta baka.

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Taɓa ɗakin Ka'aba na ɗaya daga cikin hidimomin da mahajjata kan yi

Darasi

Daya daga cikin darussan da Farouk ya koya shi ne ƙin amincewa da shaidar da mutane ke ba kamfanoni a shafukan sada zumunta.

"A fahimta ta, yawancin kamfanoni na jabu suna biyan kuɗi masu yawa ga mutane don rubuta sharhi masu kyau na karya"

Alkaluma na gwamnatin Saudiyya sun nuna cewa a shekarar da ta gabata adadin mahajjata ya zarce miliyan 1.8, inda kashi 90% daga cikinsu suka fito daga ƙasashen waje.

Mai magana da yawun hukumar Hajji da Umra ya shaida wa BBC cewa ɓullo da manhajar Nusuk ya rage yawan sayar da kujerun aikin hajji na bogi, saboda manhajar na ɗaukar bayanan mahajjata daga ƙasashe sama da 126 kuma ta tantancesu.

.

Asalin hoton, Getty Images

People are also reading