Home Back

TSADAR RAYUWA: Hauhawar farashin kaya a Kano ya jefa Kanawa cikin halin ƙaƙanikayi

premiumtimesng.com 3 days ago
TSADAR RAYUWA: Hauhawar farashin kaya a Kano ya jefa Kanawa cikin halin ƙaƙanikayi

Duk da an daɗe ana fama da raɗaɗin tsadar rayuwa, an shafe kwanaki 30 cif a Kano, kusan kowa ya manta da matsalolin hauhawar farashi, an maida hankali kan ruɗanin da ya dabaibaye masarautar Kano, bayan rushe masarautu biyar da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi.

Maida Kano a ƙarƙashin masarauta ɗaya tare da maida Sarki Muhammadu Sanusi II kan mulkin sa, ya haifar da ka-ce-na-ce na ce, ba a Kano kaɗai ba, har a faɗin ƙasar nan.

Sai dai kuma makonni biyu bayan lafawar ruɗanin, jama’a sun shiga taitayin rayuwar su, inda ake fuskantar tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci da kayan masarufi.

Halin da ake ciki ba ya buƙatar wani nazari mai zurfi ko zaman ɗaukar darasi. Kuma ba ya buƙatar sai an shiga kasuwa domin tantancewar ƙwaƙwaf.

Furucin wasu yara biyu kaɗai ya wadatar mutum ya gane cewa lallai a Kano, kamar a sauran garuruwa da yankunan karkara duk an shiga gararin tsadar rayuwa da hauhawar farashi.

Bashir na zaune ƙofar gidan su a ranar Juma’a, sai wani ɗan uwan sa daga ƙauye ya kira shi suka gaisa. Daga nan sai ya tambayi Bashir, “shin ina dokin nan na gidan ku wanda figa wa zangarniyar dawa, cikin kwana uku ya cinye dame ɗaya?”

Sai Bashir ya ce masa, “wane doki kuma? Ai tuni Baba ya rabu da dokin, saboda tsadar rayuwa. Wa zai iya riƙe doki yanzu? Dawa kuwa ai ko mu yanzu nema take ta fi ƙarfin mu, ba wai maganar a figa wa doki ya ci ba.” Inji Bashir.

Shi kuwa Muktar yaro ne da bai wuce shekaru 13 ba. Cikin sauri ya fito ƙofar gida, ya samu mahaifin sa ya ce masa, “Baba ashe idan aka zuba wa dusar awara manja aka barbaɗa maggi akwai daɗi!”

Mahaifin ya na cikin mutane, sai ce masa ya yi, “kai, don gidan su ai ba a faɗa cikin mutane.”

A wani sabon katafaren kantin zamani (Super Market) da ke mahaɗar titin Karkasara da Sallare, a Kano, Khalil ya shiga da nufin zai sayo abin da ya sauƙaƙa. Amma tun da ya ƙyalla ido ya ga farashin kifin gwangwaje ya dangwali Naira 1,200, gaba ɗaya sai ma ya fasa sayen komai, ya koma gida da kuɗin sa Naira 23,000 cikin aljihu.

“Rabo na da cin doya tun da farashin wadda na ke saye Naira 10,000.00 ya koma Naira 36,000.00. Gaskiya ba zan iya wannan jidalin ba.” Cewar Alhaji Muhammadu, wanda ya ce shi yanzu garin Kura ya ke zuwa duk ƙarshen wata ya sayo shinkafar Hausa, wadda ya ce kafin Corona bai taɓa sayen ta ya kai gidan sa ba.

Wannan masifa kuwa ba ta bar talakawa ba, kuma ba ta bar attajirai ba. Ta shafi kowa, yaro da babba, har ma da almajirai masu jiran ‘Allah ya ba ku mu samu.’

People are also reading