Home Back

El Rufai vs Uba Sani: Majalisar Kaduna Ta Bankado Shirin Mukarraban Tsohon Gwamna

legit.ng 2024/8/21
  • Majalisar jihar Kaduna ta caccaki mukarraban tsohon gwamnan jihar Kaduna kan zarginsu da ake da badakalar kudi
  • Majalisar ta yi fatali da korafinsu na cewa akwai kura-kurai a cikin rahoton binciken gwamnatinsu da ta shude
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin Nasir El-rufai da Gwamna Uba Sani a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Majalisar jihar Kaduna ta yi zazzafan martani ga mukarraban tsohon gwamna, Nasir El-Rufai kan zargin badakala.

Majalisar ta ce ba gudu ba ja da baya kan rahotonta game da zargin El-Rufai game da karkatar da N423 lokacin mulkinsa.

Majalisar Kaduna ta yi martani kan badakalar N423bn da ake zargin El-Rufai
Majalisar Kaduna ta sha alwashin ci gaba da binciken Nasir El-Rufai. Hoto: @elrufai, @ubasanius. Asali: Twitter

Majalisar Kaduna ta yi martani ga El-Rufai

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin binciken Majalisar, Henry Magaji ya fitar, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Magaji wanda shi ne matamakin shugaban Majalisar ya ce sun samu labarin sanarwar da mukarraban El-Rufai suka fitar kan zargin badakala.

Ya ce mukarraban sun ce sun gano wasu kura-kurai a cikin rahoton da ake zarginsu a kai na hamdame makudan kudi.

"Idan har su masu gaskiya ne da ya kamata su kawo ci gaba a jihar madadin fakewa da kuma karkatar da makudan kudin jihar."

"A cikin sanarwar da suka fitar, sun ce akwai kura-kurai a rahoton inda suke bata sunan Majalisar da kuma zargin shirinta na bincikensu."

"Babu wani abin da zamu yi martani a kai na wannan korafi na su tun da sun gagara yin magana kan babbar maganar da ake zarginsu a kai."

Henry Magaji

El-Rufai ya shiga sukar gwamnatin Uba Sani

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi martani bayan wani ya caccaki gwamnatin Uba Sani.

El-Rufai ya yi martanin ne bayan wani mai amfani da shafin X ya wallafa hotuna da ke kushe gwamnatin da rashin katabus.

'Yan Najeriya da dama sun yi martani bayan yada wallafar da El-rufai ya yi inda wasu suke korafin cewa shi ya ma yana da laifuffuka.

Asali: Legit.ng

People are also reading