Home Back

Kwango: Matsalar cin-hanci da rashawa

dw.com 2024/6/15
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Felix Tshisekedi | Shugaban Kasa
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

'Yan fafutukar yaki da cin-hanci da rashawa sun ce rashin hukunta shugabannin siyasa da ake zargi da almundahana na haddasa bazuwar wannan mummunar dabi'a da ke sa al'umma rayuwa cikin talauci. Kalmar almubazzaranci ta zama ruwan dare a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango tun shekara ta 2020, lokacin da aka yanke wa Vital Kamerhe shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Félix Tshisekedi hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bayan da aka same shi da laifin sama da fadi da kusan miliyan 50 na dalar Amurka a wani aiki na gina gidaje masu saukin kudi. Sai dai kotu ta wanke shi shekaru biyu bayan da ya daukaka kara, lamarin da ya ba shi damar komawa gwamnati. Watakila ya zama kakakin majalisar dokokin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, idan aka gudanar da zaben neman wannan mukami a ranar 18 ga wannan wata na Mayun da muke ciki.

Karin Bayani: Dakarun SADC sun tunkari 'yan tawayen M23

Baya ga wannan ma, akwai wasu jerin badakalolin almundahana da aka bankado ciki har da wacce ta shafi shirya wasannin guje-guje da tsalle na kasashe rainon Faransa wato Francophonie a 2023, inda aka zargi ministan kudi na yanzu Nicolas Kazadi da kuma daraktan kwamitin shirya wasannin Isidore Kwandja da almubazzaranci da dukiyar al'umma. Sai dai har ya zuwa yanzu, ba a bude wani bincike a fannin shari'ar da aka kaddamar domin gano gaskiyar maganar ba. A yayin da zaben gama-gari da aka gudanar a karshen shekarar 2023, shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kwangon Céni Denis Kadima ya zargi kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Kwango da yin sama da fadi a kudin sayan wasu kayayyakin zabe. A baya-bayan nan ma dai, an sake zargn ministan kudi Nicolas Kazadi da ya wuce kima na kudi a aikin haka rijiyoyin burtsatse a yankin Kinshasa.

Kakakin majalisar dokoki mai barin gado Christophe Mboso da kuma takwaransa da ke shugabantar majalisar dattawa Modeste Bahati Lukwebo na fuskantar zargin yin sama da fadi, a kwangilar sayo motocin da suka hada da bus 12 da kananan motocin bus 14 a kan dalar Amurka miliyan 90. Sai dai majalisun biyu sun yi watsi da wannan zargi, ba tare da kotu ta yi gaggawar bude bincike ba. Valery Madianga da ke shugabantar cibiyar bincike a harkokin kudi da ci-gaban kasa ya bayyana cewar, matsala yaduwar cin hanci da rashwa a Kwango na da nasaba da rashin kulawa saboda tsare-tsaren lura da kasafin kudin ba sa aiki yadda ya kamata.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na sahun farko na kasashen da suka fi arzikin karkashin kasa a duniya, amma kuma al'ummarta na ryuwa hannu-baka hannu-kwarya sakamakon cin-hanci da ta yi kaurin suna a kai. Hasalim am dai kasar ta kasance cikin kasashe biyar da suka fi talauci a duniya, a cewar Bankin Duniya. A shekara ta 2023 bankin ya bayyana cewar, kusan sama da kaso 74 na al'ummar kasar na rayuwa da kasa da dalar Amurka biyu da senti 15 a kowace rana. Babban sakataren kungiyar Licoco Ernest Mpararo ya dage kan mahimmancin tsarin shari'a mai zaman kansa, domin yaki da cin-hanci da rashawar. Duk kokarin da tashar DW ta yi  domin jin ta bakin ministar shari'a ta Kwango Rose Mutombo Kiese domin fahimtar dalilin da suka sa almubazzaranci da dukiyar kasa ke karuwa ya ci tura.

People are also reading