Home Back

Me Ya Sa Zumunci A Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Yake Da Danko Matuka

leadership.ng 2024/7/5
Me Ya Sa Zumunci A Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Yake Da Danko Matuka

A kwanakin baya ta yanar gizo, shugaban kasar Equatorial Guinea, Mr. Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, wanda ya yi ziyarar aiki a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, ya gana da wakilan malamai da dalibai na wata makarantar firamare da ke gundumar Jinping ta lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. 

To, amma ina dalilin ganawar? 

Ashe, a yayin ziyarar da shugaban ya kawo kasar Sin a watan Afrilun shekarar 2015, a madadin gwamnatin kasarsa ya sanar da samar da gudummawar kudi don a gyarawa, da fadada wata makarantar firamare da ke gundumar Jinping, don nuna godiya ga kasar Sin bisa yadda ta dade tana taimakawa kasarsa wajen tabbatar da bunkasuwa. Bayan shekara guda, an kammala gina wani gini mai bene biyar a makarantar, matakin da ya kyautata yanayin karatu ga yaran wurin. Don tunawa da dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu kuma, an gyara sunan makarantar ya zama makarantar sada zumunta a tsakanin Sin da Equatorial Guinea. A cikin shekaru 9 da suka gabata, sama da yara 2000 sun kammala karatu a makarantar.

A hakika, kasar Equatorial Guinea kasa ce mai tasowa wadda ba ta da wadata, amma a yayin da ita kanta ke bukatar taimako, sai ga shi ta samar da gudummawa ga kasar Sin, kuma wannan ba shi ne karon farko na hakan ba, duba da cewa tun a shekarar 2008 a yayin da mummunar girgizar kasa ta afkawa kasar Sin, kasar ta Equatorial Guinea ta samar da gudummawar kudin EURO miliyan biyu ga kasar Sin.

Tabbas abu ne da ya ratsa zukatanmu, kuma ba a rasa irin wadannan labarai da suka faru a tsakanin Sin da kasashen Afirka. To, amma me ya sa Sin da kasashen Afirka suke da zumunci mai danko kamar haka? 

Lallai kasancewar kasar Sin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce mafi yawan kasashe masu tasowa, bangarorin biyu sun fuskanci makamantan abubuwan da suka faru gare su a tarihi, suna kuma da buri kusan iri daya da suke neman cimmawa, hakan ya sa dankon zumunci a tsakaninsu ya yi ta karfafa, kuma suke hada kai da juna don tabbatar da makomarsu ta bai daya. Idan ba a manta ba, a shekarun 1960 zuwa na 1970, Sinawa sama da dubu 50 sun hada kai da al’ummar Afirka wajen gina hanyar dogo ta Tanzania da Zambia, inda suka zubar da gumi da jini, har ma suka sadaukar da rayukansu, layin dogon da ya zama alamar zumunci a tsakaninsu. A shekarar 1971 kuma, kasashen Afirka sun bai wa kasar Sin babban taimako wajen mayar da ita kan kujerarta a MDD, inda daga cikin kasashe 23 da suka gabatar da shawarar, 11 sun kasance kasashen Afirka, baya ga kuri’u 76 da aka kada na nuna amincewa, wadanda a cikinsu wasu 26 kasashen Afirka ne suka kada. Yayin da aka shiga sabon karnin da muke ciki, huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ma sai karfafa take ta yi. A shekarar 2000, bangarorin biyu sun kafa dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a takaice, dandalin da ya zamanto muhimmin tsari na yin shawarwari, da kuma hadin gwiwa a tsakanin su cikin shekaru 24 da suka gabata, tare da samar da nasarorin a zo a gani.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping yana dora matukar muhimmanci a kan cudanyar Sin da kasashen Afirka, wanda bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar a shekarar 2013, da kuma sake zabarsa a shekarar 2018, ya kai ziyararsa ta farko a matsayin shugaban kasa duk a nahiyar Afirka. Baya ga haka, ya kuma gabatar da manufar da ya kamata a bi wajen hulda da kasashen Afirka, wato nuna sahihanci, da samar da hakikanin sakamako, da kauna da kuma rikon gaskiya, don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakaninsu.

A jawabin da ya gabatar a yayin ziyararsa a kasar Tanzania a shekarar 2013, ya ce, “kasar Sin ta samar da gudummawa ga kasashen Afirka gwargwadon karfinta, kuma godiya take ga kasashen Afirka, da ma al’ummarsu bisa ga goyon baya da ma taimako da suka dade suna ba ta. A kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar juna, kullum matsayinmu a bayyane yake, wato muna tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan juna.” Furucinsa ya bayyana ainihin zumunci dake tsakanin sassan Afrika da Sin. (Lubabatu)

People are also reading