Sarautar Kano: Sanusi II ya fadi kokarin Abba Kabir bayan barnar da Ganduje ya tafka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan rigimar sauratar Kano da ake ciki.
Sanusi II ya ce mayar da shi karagar sarautar jihar gyara ne kan barnar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya yi.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin wata hira na musamman da jaridar The Sun a Kano.
Ya ce Kano ta shafe fiye da shekaru 1000 kuma babu wanda ya bukaci karin masarautu tsawon wannan lokaci.
"Mutanen Kano daya ne, basu bukaci karin masarautu ba, muna fama da matsala ce wanda wani ya rarraba mu."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba kundin tsarin mulkin Najeriya ba ne ya samar da masarautun Kano, suna nan tun kafin Najeriya, tun kafin jihadin Danfodiyo."
"Sun rike wannan sarauta na tsawon shekaru huɗu, sabon gwamna ya zo ya ce dole zai dauki mataki kan farmaki kan al'adunmu."
- Muhammadu Sanusi II
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta ci tarar gwamnatin jihar N10m kan rigimar sarauta.
Kotun ta dauki wannan matakin ne bayan gwamnatin jihar ta ba da umarnin cafke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Daga bisani, kotun ta yi fatali da bukatar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan tuge Sanusi II daga karagar sarauta.
Asali: Legit.ng