Home Back

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta zargin gididdiba burtalai a wasu garuruwan ta uku

dalafmkano.com 2024/5/19

Ƙaramar hukumar Tofa ta musanta batun gididdiba burtalai a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, dukka a ƙaramar hukumar da ake zargin an siyarwa Manoma, domin suyi aikin Noma.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan a daren jiya Laraba, lokacin da yake tsokaci kan koken da Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka yi, kan yadda suka zargi an gididdiba burtalai a yankunan su, an siyarwa wasu Manoma, domin suyi aikin Noma, lamarin da suka ce hakan barazana ce a gare su.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu wajen gididdiba burtalai a garuruwan, yana mai cewa ko da kansilolinsa daga zuwan su bai taɓa sanin wanda ya siyar da koda kuwa kunya ɗaya ba a cikin shugabancin sa na ƙaramar hukumar domin ayi Noma, haka shima bai siyar ba.

“Yanzu haka ana kan ɗaukar matakin doka akan waɗanda suka fitar da al’amarin, kasancewar maganar tana wajen ƴan sanda, kuma ana faɗaɗa bincike, “in ji shi”.

A ziyarar gani da Ido, da tashar Dala FM Kano, ta kai wasu daga cikin burtalan da aka yi zargin an siyarwa Manoman, ta iske yadda wasu mutane suke share guraren, kamar yadda suka shaida cewa waɗanda aka siyarwa ne suka basu aikin share wajen.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, wannan na zuwa ne bayan da wasu Fulani Makiyaya mazauna garuruwan suka koka, bisa yadda suka ce an gididdiba burtalai a yankunan su, duk da wani manomi yace har takarda aka bashi bayan an siyar masa, lamarin da ya sa su cikin damuwa bisa yadda hakan ka iya sanyawa su rasa guraren da za su yi kiwon Shanun su.

People are also reading