Home Back

Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya ciwo bashin Dala miliyan 500, domin aikin kafa mitocin wutar lantarki a gidan kowa

premiumtimesng.com 2024/6/26
DALA BILIYAN 18: Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin binciken kwangilar gina Centenary City a Abuja

Majalisar Dattawa ta amince wa riƙon da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi mata a rubuce, domin ta yarda ya ciwo bashin Dala miliyan 500, kuɗaɗen da za a sayo mitocin wutar lantarki da su, waɗanda za a kafa a gidaje, shaguna da wuraren muhalli daban-daban a faɗin ƙasar nan.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ne ya jagoranci zaman majalisa kuma ya yi sansrwar, bayan mafiya yawan dattawan majalisar sun amince da buƙatar ta Shugaba Tinubu.

Majalisa ta amince da karɓo lamunin Kwamitin Lura da Basussukan Cikin Gida da na Waje ya gabatar da rahoton sa, wanda Mataimakin Shugaban Kwamiti, Haruna Manu ya gabatar.

Wannan bashi na Dala miliyan 500 ya na cikin basussuka na Dala biliyan 7.94 da na fam miliyan 100 waɗanda Shugaba Tinubu ya nemi amincewa zai karɓo a cikin Nuwambar da ya gabata.

Sanata Manu ya ce tun tuni ya kamata a ce an amince a ciwo bashin, amma an samu latti da jinkiri ne saboda jami’an Hukumar BPE ba su bayyana gaban Kwamiti domin su kare cancanta a haƙiƙanin hujjojin gaskata aikin da za a yi da kuɗaɗen ba.

Ya tabbatar da cewa irin sharuɗɗa da ƙa’idojin da ke tattare da karɓo lamunin, ba zai yiwu wasu su yi wa bashin asarƙala ba.

Ya ce karɓo bashin da kuma yin amfani da shi zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

People are also reading