Home Back

Kawancen jam'iyyun CDU/CSU na kan gaba a zaben EU

dw.com 2024/7/5
Wata mai kada kuri'a a zaben majalisar dokokin EU
Wata mai kada kuri'a a zaben majalisar dokokin EU

Sakamakon farko na zaben majalisar Turai, na nuna cewa kawance jam'iyyun CDU/CSU a Jamus na kan gaba a fafatawar da ake yi na zaben majalisar dokokin Turan da kimanin kashi 30%.

Jam'iyyar AfD ta masu akidar kyamar baki kuwa ta kasance ta biyu da kashi 16% a zaben da aka yi a Jamus din. Sakamkon dai ya nuna hadakar jam'iyyun shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ba su yi abin a zo a gani ba.

Kimanin Jamusawa milyan 360 ne za su kada kuri'unsu a zaben, wanda ke kasancewa zaben gama-gari na farko da 'yan kasar za su zabi mambobin majalisar dokoki baya ga zaben 2021 da 2025 da ke tafe.

Alkaluman farko na nuna jam'iyyar Shugaban gwamnatin Jamus Scholz SPD ta samu kaso 15 cikin 100, kasa da kashi 25.7 cikin 100 da jam'iyyar ta samu a zaben 'yan majalisar dokokin kasar a 2021. Lamarin dai bai yi wa kawancen jam'iyyun da ke tare da jam'iyyar SPD ta Mr. Scholz dadi ba. A jamlace kawancen jam'iyyun da suka hada da jam'iyyar the Greens da liberal Free Democrats (FDP), sun sama kashi 35%.

A bangaren adawa kawancen jam'iyyun CDU da CSU sun yi samu gagarumar rinjaye da yawan kuri'u da ya kai kashi  30% a zaben EU, yayinda jam'iyyar AfD da ke kasancewa ta biyu a da'irar siyasar Jamus ta samu kashi 14%.

People are also reading