Home Back

N3.3tr: Kamfanin NNPC Ya Yi Maganar Zargin Aringizon Kudin Tallafi a Lokacin Buhari

legit.ng 2024/7/2
  • Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya yi magana kan zargin cuwa-cuwar makudan kudin tallafi a gwamnatin da ta gabata
  • An zargi kamfanin da yin karin kudin tallafin man fetur har Naira tiriliyan 3.3 a lokacin mulkin Muhammadu Buhari
  • Mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye ne ya bayyana gaskiyar abin da ya faru a jiya Litinin, 10 ga watan Yuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kamfanin mai na kasa NNPC ya yi magana kan zargin aringizon kudin tallafi da aka zarge shi da yi a mulkin Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye ya bayyana cewa ba ƙamshin gaskiya cikin zargin da ake yi musu.

NNPC LIMITEd
NNPC ya musa yin sama da fadi da kudin tallafin mai. Hoto: NNPC Limited Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wata sanarwar da kamfanin NNPC ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"NNPC bai karkatar da kudin tallafi ba"

Mai magana da yawun NNPC, Olufemi Soneye ya ce dukkan harkokin kudi da kamfanin ya yi suna nan a rubuce kuma za a iya bincike a kansu.

Saboda haka ya ce kamfanin ya yi Allah wadai da zargin da aka masa na karkatar da kudi sama da Naira triliyan 3.

Soneye: "NNPC na yin komai a bayyane"

Har ila yau, Olufemi Soneye ya ce kamfanin NNPC ba ya rufa-rufa kan gudanar da harkokin kasuwanci.

Kuma kamfanin na tafiyar da harkokinsa a bisa tsarin zamani ta yadda ba zai bar kofar yin aringizo da kudin tallafi ba.

Kamfanin NNPC ya shawarci 'yan jarida

Olufemi Soneye ya ce abin takaici ne yadda wasu kafafen yada labarai suka wallafa labarin ba tare da tantancewa ba.

A karkashin haka ya shawarci yan jarida da su rika tuntubar hukumomi domin jin yadda lamura suke kafin wallafawa.

MENAN ta yi magana kan kudin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar manyan dillalan mai ta kasa (MEMAN) ta ƙaryata rahoton cewa za a dawo sayar da litar fetur kasa da N300.

Rahotanni sun tabbatar da cewa MEMAN ta ce sai gwamnati ta fifita matatun cikin gida wajen samar masu da danyen mai hakan zai tabbata.

Asali: Legit.ng

People are also reading