Home Back

Majalisar Faransa ta yi tur da kisan da aka yi wa 'yan Algeria a 1961

rfi.fr 2024/4/29

Majalisar Wakilan Faransa ta amince da kudirin da ke yin Allah-wadai da kisan kiyashin da ‘yan sandan kasar suka yi wa gomman ‘yan Algeria a shekarar 1961 lokacin da suke zanga-zangar goyon bayan ‘yancin kasarsu ta arewacin Afrika.

Wallafawa ranar: 28/03/2024 - 17:58

Minti 1

Lokacin da jami'an 'yan sandan Faransa suka tsare 'yan Algeria a birnin Paris a shekarar 1961.
Lokacin da jami'an 'yan sandan Faransa suka tsare 'yan Algeria a birnin Paris a shekarar 1961. © AFP/Fernand Parizot

A shekarun baya-bayan nan Faransa na ta yunkurin ganin ta gyatta alakarta da Algeria dangane da jerin cin zarafin da suka faru a lokacin mulkin mallakar da ta yi wa kasar ta arewacin Afrika, sai dai duk da hakan an gaza kai ga jituwa tsakanin bangarorin biyu.

Daruruwan ‘yan Algeria da ke zanga-zangar goyon bayan ‘yancin kan kasar a  shekarar 1961 ne suka rasa rayukansu bayan da ‘yan sandan Paris suka bude musu wuta a wani yanayi da aka bayyana da kisan kiyashi lamarin da tun a shekarar 2021 shugaba Emmanuel Macron ya amsa laifin kasarsa  tare da neman afuwar Algria game da abin da ya faru.

A general view shows the hemicycle as members of parliament react after the vote on a motion to dismiss the text before a debate on immigration law at the French National Assembly in Paris, France, De
Zauren Majalisar Dokokin Faransa REUTERSFR - STEPHANIE LECOCQ

Daftarin kudirin wanda jam’iyyar Greens karkashin jagorancin Sabrina Sebaihi ta gabatar gaban majalisar ya samu goyon bayan ‘yan majalisa 67 wasu 11 kuma suka kalubalance shi.

Bayan nasarar da kudirin ya samu a zauren majalisar, ‘yar majalisa Sabrina ta bayyana nasarar da matakin farko wajen ayyana kisan kiyashin a matsayin laifi marar muni da ‘yan sandan na Faransa suka aikata kan al’ummar Algeria.

Yayin gangamin cika shekaru 60 da aikata kisan kiyashin da ya gudana a shekrar 2021, shugaba Macron da kansa ya amsa cewa tarin masu zanga-zangar da ‘yan sandan na Faransa suka kashe a wancan lokaci sun jefa gawarwakinsu a cikin rijiya.

 
People are also reading