Home Back

RUGUJIN YAƘI A ZAMFARA: Yadda ‘Yan bindiga 12 suks sha wuta yayin gumurzu da sojoji cikin Dajin Ɗansadau

premiumtimesng.com 2024/5/14
TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

Zaratan Sojojin ‘Operation Hadarin Daji’ (OPHD) sun ratattake ‘yan bindiga 12 tare da ƙwato makamai, a wani gumurzu da suka yi cikin Dajin Ɗansadau.

Jami’in Yaɗa Labaran OPHD, Suleman Omale ne ya bayyana wa manema labarai haka, a cikin wata sanarwar da ya fitar, ranar Asabar a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Laftanar Omale ya ce sojoji sun samu wannan nasara ce saboda ci gaba da kai wa mahara farmakin da su ke yi har can cikin dazukan da suke a ɓoye, domin ganin an kakkaɓe su, kuma an samu zama lafiya a yankin.

Omale ya ce dakarun sojoji sun mamaye yankunan Babban Doka, Gobirawar Challi da Kabaro, a cikin Ƙaramar Hukumar Maru, bayan sun kakkaɓe mahara a gumurzun da suka kashe 12 daga cikin su.

Ya ce an yi wannan fafatawar ce a ranar Juma’a.

“Lokacin fafatawar da sojojin mu daga Dajin Ɗansadau, sun nuna jarunta, domin sun tanƙware ‘yan bindiga, tare da kashe 12 daga cikin su, wasu kuma su ka arce bayan sun samu raunuka a jikin su.

“A ci gaba da farmakin, sojojin mu sun ƙwato makamai masu yawa, ciki har da AK-47 guda ɗaya, albarusai da yawa.

“An kuma yi nasarar ƙwato shanun mutane har gida 12, babura guda 10, waɗanda nan take aka banka masu wuta.

People are also reading