Home Back

Borno: Majalisar Dattawa Ta Faɗi Sakacin da Ya Jawo Aka Kai Harin Bam a Gwoza

legit.ng 3 days ago
  • Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta umarci sojoji su sauya salon yaƙi da ƴan tada kayar baya a Najeriya
  • A zaman ranar Laraba, 3 ga watan Yuli, majalisar ta ɗora alhakin harin bam da aka kai a Gwoza kan sakacin tattara bayanan sirri
  • Ta ce lokaci ya yi da jami'an tsaron Najeriya za su shigo zamani, su fara amfani da dabarun kimiyya da fasaha wajen kakkaɓe ayyukan ta'addanci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar dattawa ta dora alhakin harin kunar bakin wake da aka kai a garin Gwoza na jihar Borno a kan gaza tattara bayanan sirri daga bangaren jami’an tsaro.

Shugaban majalisar Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a yayin muhawara kan kudirin da mai tsawatarwa Sanata Ali Ndume, ya gabatar a zaman ranar Laraba, 3 ga watan Yuli.

Majalisar dattawan Najeriya.
Majalisar dattawa ta ɗora alhakin harin bam da aka kai a Gwoza kan sakacin tattara bayanan sirri Hoto: @NGRSenate Asali: Facebook

Tun farko a jawabinsa, Ndume ya ce har yanzun ƴan ta'adda na da mafaka a tsaunin Mandara, dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A matakan da ta ɗauka kan kudirin, majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta umurci sojoji da su sake lalubo dabarun yaƙi da ƴan tada ƙayar baya.

Ta bukaci dakarun sojoji su canza dabarun tunkarar ƴan ta'adda, su koma amfani da fasahar zamani da dabarun kimiyya domin tabbatar da zaman lafiya.

Sanatocin sun lura cewa dogaro da hanyoyin da kowa ya sani wajen tunkarar ƴan tayar da ƙayar baya kamar tura dakarun sojoji ba kasafai ake samun nasara ba.

A cewar majalisar dattawan, tsayawa kan waɗannan hanyoyi na karfin soji kaɗai na ci gaba da bai wa ƴan ta'adda damar ɓullo da wasu hanyoyin da ba a yi zato ba a yanzu.

Ta ce hakan na jawo asarar rayukan ƴan Najeriy da dukiyoyinsu, wanda ya kamata hukumomin tsaro su taka wa lamarin birki.

Tinubu ya naɗa mace a shugabar FGSHLB

A wani rahoton Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Hajiya Salamatu Ladi Ahmed a matsayin sabuwar babbar sakatariyar hukumar ba da lamuni FGSHLB.

Shugaban ƙasar ya tabbatar da wannan naɗi ne ta hannun shugabar ma'aikatan tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan ranar Talata a birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

People are also reading