Home Back

Kasar Sin Ta Ware Kudi Domin Gyaran Titunan Da Ambaliya Ta Lalata

leadership.ng 2024/7/1
Kasar Sin Ta Ware Kudi Domin Gyaran Titunan Da Ambaliya Ta Lalata

Ma’aikatar harkokin kudi ta kasar Sin, ta ce kasar ta ware jimilar yuan miliyan 105, kwatankwacin dala miliyan 14.7 domin tallafawa gaggauta gyaran titunan da ambaliyar ruwa ta lalata.

Ma’aikatar ta bayyana a jiya cewa, za a yi amfani da kudin nan take, domin gyara titunan da suka lalace sanadiyyar ambaliya a lardunan Guangdong da Guangxi da Zhejiang da Fujian da Jiangxi da Hunan da kuma Guizhou, tare da tabbatar da zirga-zirga cikin aminci yayin da ake cikin lokacin ambaliya.

Yankunan kudancin kasar Sin da dama na fama da zubar ruwan sama akai-akai a wannan lokacin zafi na bana, lamarin da ya haifar da lalacewar tituna da gine-gine, tare da rutsawa da mutane. (Fa’iza Mustapha)

People are also reading