Home Back

‘Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Abuja Zuwa Nasarawa

leadership.ng 2024/7/1
‘Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Abuja Zuwa Nasarawa

‘Yan bindiga sun sace wasu fasinjoji da ke kan hanyarsu ta zuwa Abuja daga Jihar Enugu, bayan da suka kai wa motar safa mai cin fasinja 18 hari a Jihar Nassarawa.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Nassarawa, Dsp Ramhan Nansel ne, ya bayyana hakan ga manema labarai.

Nansel, ya ce ‘yansanda sun samu bayanin cewar an kai wa wata motar safa mai cin mutane 18 da ke kan hanyarta ta zuwa Abuja daga Jihar Enugu hari a kauyen Doruwa, da ke kan hanyar Nassarawa zuwa Keffi tare da yin garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba.

Ya kara da cewar daga bisani an yi nasarar kubutar da mutane uku daga cikin mutanen bayan da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro suka kaddamar da samame a yankin.

Ya kara da cewar, “yansanda, da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun kaddamar da samamen gaggawa, saidai harin ya riga ya faru gabanin su samu labari.

“An bi sahun ‘yan ta’addar tare da karade yankin. Sakamakon hakan, an yi nasarar kubutar da mutane uku, tare da kwato wasu ababen hawa.”

Nansel ya bayar da tabbacin cewar hukumomin tsaro ba za su saurara ba, kuma za su ci gaba da aikin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

People are also reading