Home Back

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/07/2024

bbc.com 2 days ago

Rahoto kai-tsaye

An shiga rana ta ƙarshe a yaƙin neman zaɓen Birtaniya

.

Asalin hoton, PA/Reuters

'Yan siyasa a Birtaniya na gangamin yaƙin neman ƙuri'u a rana ta ƙarshe a jajiberen zaɓen da za a yi a gobe.

Jam'iyyar Labour na kan gaba a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a a lokacin yaƙin neman zaɓen da aka ɗauki mako shida ana yi.

Firaminista Rishi Sunak ya jima yana gargaɗin masu kaɗa ƙuri'a kada su bai wa jagoran 'yan adawa Keir Starmer, damar yin rinjaye a majalisa.

Jam'iyyar Labour ta sha kaye a zaɓuka huɗu, dan haka Sir Keir ya buƙaci magoya baya su tabbatar sun kaɗa ƙuri'a a gobe Alhamis.

Tsohuwar sakatariyar harkokin gida ƙarƙashin jam'iyyar Conservative, Suella Braverman, ta ce yawancin 'yan ga-ni-kashe-nin jam'iyyar na komawa jam'iyyar Reform UK, saboda tsattsauran ra'ayinsu kan batun 'yan cirani.

People are also reading