Home Back

Faransa ta wahala wajen doke Ostiriya a gasar Euro 2024

dw.com 2024/7/7
 Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa kwallo a karawar da ta yi da Ostiriya
Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa kwallo a karawar da ta yi da Ostiriya

Za a iya cewa dara ce ta ci gida domin akasin da aka samu bayan da dan wasan baya na Ostiriya Maximilian Wöber ya buga kwallo da ka a bangaren da ba ta dace ba, amma shahararren dan wasan Faransa Kylian Mbappé ya tsinci dami a kala inda ya ci daya dayan kwallo. Sai dai dan wasan baya na kungiyar les Bleus na Faransa Jules Koundé ya ce ko da Faransa ba ta taka rawar gani a fada ba, amma kwalliyarta ta biya kudin sabulu domin ta samu maki uku

Koundé ya ce: "Ina ganin cewar mun buga wasa mai kyau. Amma an samu zazzafan martani daga abokan hamayya. Mun samu damammaki masu yawa, amma da mun kara azama da abubuwa sun zo mana da sauki. Sai dai na gamsu da wasan."

Salon wasan Ostiriya bai kayatar ba

'Yan wasan Ostiriya sun shafe tsawo mintuna 90 suna gwada kwanji da takwarorinsu na Faransa maimakon amfani da dabaru wajen zura kwallo a raga. Saboda haka ne wasu daga cikin 'yan wasan Ostiriya ke nadamar salon wasa da suka runguma, lamarin da ke iya zama izina ta wasannin da za su buga a gaba, a cewar Philip Mwene dan wasan gefe na Ostiriya.

Ya ce: "Ko yaushe ina jin takaici bayan shan kaye a wasa. Ina ganin cewa duk da rashin nasara, yadda muka tunkari wasan da kuma yadda muka taka leda na ba ni kwarin gwiwa game da wasanni na gaba."

Ostiriya za ta kara wasanta na gaba da Poland, yayin da Faransa za ta yi karon batta da Netherlands ko Holland a rukunin D. Sai dai yanayi na rashin tabbas ya mamaye kungiyar ta Faransa bayan da kyaftin dinta Kylian Mbappé ya fuskantar matsalar karyewar hancin, saboda haka babu tabbas ko zai yi wasa na gaba ko a'a.

Slovakiya ta ba wa mara da kunya

A bangarenta, Slovakiya ta ba da mamaki sakamakon nasarar doke Beljiyam da ta yi da ci 1-0 a birnin Frankfurt. Tun ma a minti na bakwai da fara wasa ne Ivan Schranz ya cira wa kasarsa kitse a wuta, amma kuma 'yan wasan Diable Rouges na Beljiyam suka kasa rama wa kura naiyarta. Maimakon haka ma, alkalin wasa ya soke kwallaye biyu da Romelu Lukaku ya ci. Saboda haka ne kyaftin Kevin de Bruyne ya ce lokaci ne na zage dantse domin samun nasara a wasanni na gaba:

de Bruyne ya ce: " Idan kuka yi rashin nasara a wasan farko, kun san cewar dole ne ku lashe wasa na biyu. Za mu yi iya kokarinmu don mu cimma burinmu. Za mu sake haduwa, za mu tabbatar da cewa mun yi tasiri a wasa na gaba. Ba mu damu sosai a yanzu ba."

A wasa na gaba, Beljiyam za ta kara ne da Romaniya da ke jagorantar rukunin E bayan da ta doke Ukraine da ci 3-0. Wannan wasa zai gudana a ranar Asabar da yamma a birnin Cologne. Washe gari kuma Slovakiya za ta kara da Ukraine a birnin Düsseldorf.

People are also reading