Home Back

Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Rigimar Sarauta da Aka Dade Ana Yi

legit.ng 3 days ago
  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar sarauta na tsawon shekaru, Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan makomar Michael Onakoya
  • Kotun ta yi fatali da korafin Onakoya inda ta tabbatar da tsige shi a matsayin sarkin Igbooye da ke Ipe a jihar Lagos
  • Wannan na zuwa ne bayan basaraken ya daukaka kara a Kotun Koli bayan rasa kujerar a Kotun Daukaka Kara da kuma kotun jihar Lagos

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Kotun Koli ta tabbatar da korar Sarkin Igbooye da ke Ipe, Michael Onakoya daga kujerar sarauta a jihar Lagos.

Kotun ta yi fatali da korafin da Onakoya ya yi inda yake kalubalantar tube shi a kujerar sarauta da aka yi a jihar.

Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar sarauta a Lagos
Kotun Koli ta tabbatar da tsige Michael Onakoya a matsayin Sarkin Igbooye da ke jihar Lagos. Hoto: Supreme Court of Nigeria. Asali: Facebook

Hukuncin da kotun ta yi a Lagos

Mai Shari'a, Adamu Jauro shi ya yanke hukunci a karar mai lamba SC//CV//969/2024 inda ya ce korafin ba shi da inganci, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Maris din shekarar 2020, Kotun Daukaka Kara da ke Lagos ta yi hukunci inda ta tabbatar da korar sarkin daga kujerarsa.

Tun farko, Babbar Kotun jihar ne da ke Igbosere ta yi hukunci inda ta tuge Onakoya daga sarautar Igbooye a Ipe, Tribune ta tattaro.

Sarki Onakoya ya daukaka kara a kotu

Bayan hukuncin bai yi masa dadi ba, tubabben sarkin ya daukaka kara inda ya bukaci kotun ta yi fatali da hukuncin karamar kotun a shekarar 2016.

Sai dai alkalan Kotun Kotun Daukaka karar guda uku karkashin jagorancin Mai Shari'a, Mohammaed Lawal sun yi fatali da korafin Onakoya.

Sauran alkalan sun hada da Mai Shari'a, Ugochukwu Ogakwu da Mai Shari'a Jamilu Tukur inda suka ce korafin ya rasa gamsassun hujjoji.

Kotu ta dage shari'ar sarautar Kano

A wani labarin, mun kawo muku rahoton cewa Babbar Kotun jihar Kano ta dauki mataki kan shari'ar sarauta da ake yi.

Mai Shari'a, Amina Adamu Aliyu ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Alhamis 4 ga watan Yulin 2024 domin yanke hukunci.

Hakan ya biyo bayan dambarwar sarautar da ake ci gaba da yi tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Asali: Legit.ng

People are also reading