Home Back

Gwamnatin Tinubu Ta Dawo da Shirin Rage Talauci Ga 'Yan Najeriya Miliyan 75

legit.ng 2024/6/26
  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawonda shirin ba da tallafin kuɗi na kai tsaye ga ƴan Najeriya miliyan 75 a gidaje miliyan 50
  • Ministan kuɗi Wale Edun ne ya tabbatar da dawo da shirin domin rage raɗaɗi ga talakawan Najeriya masu fama da talauci
  • A baya dai gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ne bayan zarge-zargen da ake yi kan yadda ake gudanar da shirin na bayar da tallafin kuɗin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta dawo da shirin ba da tallafin kuɗi ga ƴan Najeriya.

Gwamnatin ta ce shirin zai riƙa biyan kuɗi kai tsaye ga ƴan Najeriya miliyan 75 da ke cikin gidaje miliyan 50 domin rage raɗaɗin da ƴan ƙasar ke ciki, musamman talakawa.

Gwamnati za ta ci gaba da ba 'yan Najeriya tallafin kudi
'Yan Najeriya miliyan 75 za su amfana da shirin ba da tallafin kudin Hoto: @OfficialABAT Asali: Twitter

An yi wa shirin garambawul

Gwamnatin ta bayyana cewa an yi gyaran fuska ga shirin ba da tallafin kuɗin na kai tsaye domin magance zamba, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan kuɗi Wale Edun ne ya sanar da hakan a wajen taron bayanin ministocin domin cikar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu shekara ɗaya a kan mulki a ranar Talata a Abuja.

Ministan ya kuma bayyana cewa tattalin arziƙin ƙasar nan yana ƙara haɓaka, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

A baya dai gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin bayan zargen-zargen da aka yi kan aikata rashin gaskiya a wajen gudanar da shirin.

Meyasa gwamnati ta dawo da shirin?

Da yake yin ƙarin haske kan dawo da shirin, ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar dawo da shirin domin ragewa talakawan Najeriya raɗaɗi.

"Gwamnati ta sake dawo da shirin ba da tallafin kuɗi wanda zai riƙa biyan ƴan Najeriya miliyan 75 kuɗi kai tsaye a gidaje miliyan 50."
"An ƙara inganta hanyoyin samun lamuni, inda aka ware Naira biliyan ɗaya (N1bn) domin ba da lamuni, sannan an ba da tallafin N50,000 ga ƙananan masana'antu miliyan ɗaya."

Wale Edun

Murnar cikar Tinubu shekara 1 a mulki

A baya rahoto ya zo cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin da zai ɗauki alhakin gudanar da taron bikin cika shekara ɗaya na mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Taron wanda za a gudanar domin tunawa da ranar 29 ga watan Mayu, 2023, zai waiwayi nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu a cikin shekara ɗaya.

Asali: Legit.ng

People are also reading