Home Back

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/07/2024

bbc.com 2024/8/24

Rahoto kai-tsaye

NATO ta ce za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine don ta zama mamba

nato

Asalin hoton, Getty Images

A rana ta biyu na taron ƙungiyar tsaro ta NATO da ke gudana a Amurka, ƙungiya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine don zama mamba a cikin ƙungiyar.

A sanarwar hadin gwiwa da Nato ta fitar da sakatare janar mai barin gado, Jens Stoltenberg, ya karanta, ya ce za su ba da tallafin soji na dala biliyan 40 ga Ukraine a cikin shekara guda.

An cimma yarjejeniyar ƙawancen Nato ƙarkashin jagorancin Amurka, za su taimaka wa Ukraine horas da sojinta da kai makamai.

Mista Stoltenberg ya ƙara da cewa za su taimaka wa Ukraine da abin da ya dace domin nuna wa Mista Putin ba zai yi nasara ba.

People are also reading