Home Back

Zamu baza jami’an mu 2,500 domin samar da tsaro lokacin bikin babbar Sallah, a Kano – Bijilante

dalafmkano.com 2024/6/25

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano ƙarƙashin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta ce za ta baza jami’an ta aƙalla su 2,500, domin taimakawa wajen samar da tsaro s sassan jihar yayin gudanar da bikin babbar Sallah.

Mai magana da yawun ƙingiyar Bijilanten a matakin jaha, kuma kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge Usman Muhammad Ɗa -Daji, shine ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa gidan rediyon Dala FM Kano, a daren jiya Juma’a.

Ɗan Daji, ya kuma ce jami’an su za su yi duk mai yiyuwa wajen samar da tsaro ga al’ummar jihar Kano, domin ganin an gudanar da bikin babbar sallar cikin kwanciyar hankali da lumana.

“Mutane ku fito masallatai domin gudanar da sallar Idi, da yardar Allah, babu wata matsalar tsaro da za’a fuskanta a faɗin jihar Kano, musamman ma a lokacin sallar jami’an mu za suyi duk abinda ya kamata wajen samar da tsaro, “in ji Ɗan-Daji”.

Daga bisani kuma ƙungiyar Bijilanten ta ƙasa reshen jihar Kano, ta buƙaci haɗin kan al’umma dan ganin komai ya tafi yadda ya kamata.

A gobe Lahadi 15 ga watan Yunin 2024, ne dai za ayi Idin babbar Sallar a faɗin Duniya, yayin da Alhazai a ƙasa mai tsarki suke gudanar da tsayuwar Arafah a yau Addabar, a ci gaba da gudanar da aikin Hajjin bana.

People are also reading