Rikici Ya Ɓarke Yayin da Kakakin Majalisa Ya Dakatar da Ƴan Majalisa 3, Bayanai Sun Fito
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, na jam'iyyar PDP ya dakatar da ƴan majalisa uku ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, 2024.
Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da ƴan majalisar ne saboda yunƙurin haifar da fargaba a zauren majalisar ta hanyar amfani da dodo.
Haka zalika an ɗauki matakin dakatar da mambobi uku na majalisar ne bisa zargin sun fara kulla makircin tsige kakakin majalisar da wasu jagorori.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Donald Okogbe (PDP, Akoko-Edo II), Bright Iyamu (PDP, Orhionmwon II), da Adeh Isibor (APC, Esan ta Arews maso Gabas I).
Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Honorabu Agbebaku ne ya sanar da dakatar da mambobin 3 a zaman yau Litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Mista Agbebaku ya zargi ƴan majalisar da yunƙurin ta da yamutsi a zauren majalisar da ka shirim tsige shugabannin majalisa.
Kakakin ya kuma bayyana cewa wasu mutane sun kawo bokaye zauren majalisar ranar 1 ga watan Mayu, 2024 kuma sun yi tsubbace-tsubbace kana suka bar layoyi a wurin.
Amma wannan dakatarwa ta kawo yamutsi a zauren majalisar domim nan take ƴan majalisar da matakin ya sha suka sa ƙafa suka shure dakatarwar.
A cewarsu:
"Mai girma shugaban majalisa, ba ka da damar dakatar da kowane dan majalisar haka kawai, dole ne sai kowane mamba ya kaɗa kuri'a, ka bar mambobi su kaɗa kuri'a."
Domin kawo ƙarshen tada jijiyoyin wuya tsakanin ƴan majalisar, nan take Agbebaku, ya ɗage zaman majalisar.
A wani labarin
Asali: Legit.ng