Home Back

Juventus ta kammala ɗaukar Luiz daga Aston Villa

bbc.com 6 days ago
Douglas Luiz

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar Italiya, Juventus ta kammala ɗaukar Douglas Luiz daga Aston Villa kan £42.35m.

Tuni ɗan kasar Brazil, mai shekara 26, ya saka hannu kan ƙunshin yarjejeniyar shekara biyar da ƙungiyar da ke buga Serie A.

Luiz, wanda ya buga wa kasar sa wasa 15, ya ci ƙwallo 22 a karawa 204 da ya yi wa Villa, wadda ta ɗauke shi daga Manchester City a 2019.

Yanzu haka ɗan wasan yana tare da tawagar Brazil da ke buga Copa America a kasar Amurka, inda Juventus ta kammala auna koshin lafiyarsa a can.

Luiz ya ci ƙwallo tara a wasa 35 a gasar Premier League da ta wuce, inda Villa ta kare a mataki na hudu da samun gurbin buga Champions League a kakar 2024/25.

Villa na kokarin bin dokar samun kudi daidai samu ta Premier League, hakan ya sa dole ta rabu da wa su fitatcen ƴan ƙwallonta.

Dokar ta tanadi ƙungiyar Premier League za ta iya yin asarar kasuwancin £105m a kaka uku, idan ƙudin ya haura haka ya zama da matasala kenan.

Tuni kuma Villa ta sayar da Tim Iroegbunam ga Everton kan £9m, haka kuma Chelsea ta kammala sayen Omari Kellyman kan £19 daga kungiyar Villa Park.

People are also reading