Sallah: "Ku Tuna da Wadanda ba su yi Layya ba" Malamin Addinin Islama ya Shawarci Musulmi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos- Duba da halin matsin rayuwa da ‘yan Najeriya ke fuskanta ga kuma sallah babba na tunkarowa, wani malamin addinin musulunci, Dr Tajudeen Adebayo ya shawarci musulmi kan abin da ya kamata su yi.
Dr Tajudeen Adebayo duk musulmin da ba shi da yadda zai yi domin yanka kamar yadda addini ya umarci mai hali ya yi, ka da ya shiga damuwa sosai.
Vanguard News ta wallafa cewa malamin ya bayar da shawarar ne a jihar Legas, inda ya ce duk wanda ke fama da rashin abin hannu ya dage da addu’a amma ka da ya bari bakin ciki ya lullube shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin addinin Islama, Dr Tajudeen Adebayo ya shawarcu musulmin da Allah SWT ya hore masu abin yanka da su taimakawa na kusa da su da ba su samu ikon yi ba da bikin sallah babba.
Ya bayar da wannan shawara ne ganin yadda ‘yan Najeriya su ke fama da kuncin rayuwa, yayin da kayan amfanin yau da gobe, ciki har da ragunan sallah su ka yi tashin gwauron zabo,.
” Idan matsin tattalin arziki bai baka damar yin yanka da sallan nan ba, ka da ka shiga damuwa da yawa. Akwai wata lokaci mai kyau a gaba.”
” Duk wada ya yi yanka ya raba ga wadanda ba su samu damar yi ba.”
Malamin ya tunatar da musulmi cewa jini ko naman dabbar da su ka yanka ba zai kai ga Allah SWT ba, said ai niyyar da aka yi yankan da shi, kamar yadda Daily Post ta wallafa.
A baya mun kawo muku labarin cewa asirin wasu barayin raguna ya tonu a babban birnin tarayya Abuja lokacin da su ke kokarin sayar da wasu ragunan sallah biyu da su ka sato a gidan wani bawan Allah.
An kama barayin yi kasa da awanni 48 bayan samun nasarar cafke wasu da ake zargi da satar shanu a kasuwar dabbobi ta Abaja a Abuja da niyyar cefanar da su ga masu sayen dabbar layya.
Asali: Legit.ng