Home Back

Shugaban Majalisa ya Fadi Muguwar Illar da Bukatar NLC za ta Yiwa Ma'aikata

legit.ng 2024/7/1
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya gargadi kungiyoyin kwadago da kada su manta da ma'aikatan dake aiki karkashin kamfanoni masu zaman kansu
  • Ya bayyana cewa da yawa akwaikamfanonin da ba za su iya biyan mafi karancin albashin ba, kuma hakanzai sa 'yan Najeriya da yawa su rasa aikinsu su koma zaman kashe wando
  • Kungiyoyin kwadago a Najeriya na neman gwamnatin tarayya ta amince da biyan N494,000 a matsayin mafi karancin albashi, amma gwamnati ta ce N60,000 za ta iya biya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana bukatar kungiyar kwadago ta NLC na biyan N494,000 da cewa zai jawo matsala babba ga ma’aikatan da ke aiki a kamfanonin masu zaman kansu.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin taron gaggawa kan batun mafi karancin albashi da ya gudana a yammacin Lahadi a dakin taron majalisar dake Abuja

Godswill Obot Akpabio
Mafi karancin albashi: Sanata Godswill Akpabio ya ce ma'aikata a kamfanoni za su fuskanci matsala Hoto: Godswill Obot Akpabio Asali: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa Sanata Akpabio ya hori shugabannin kungiyoyin kwadago su duba halin da bukatarsu zai jefa ma’aikatan da ba na gwamnati ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio-NLC: ‘A yi taka tsan-tsan,’

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya gargadi kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da ta ‘yan kasuwa (TUC) kan su duba bukatun ma’aikata kafinsu kafe kan mafi karancin albashi.

Kungiyoyin sun dage kan sai dai gwamnatin tarayya ta amince da N494,000 a matsayin mafi karancin albashi duba da karin kudin wuta da na man fetur, kamar yadda Punch News ta wallafa.

Da yake ganawa da NLC da takwarorinta, Sanata Akpabio ya ce ;

‘…kada mu je a garin tilasta tabbatar da mafi karancin albashi, mu fuskanci matsalar rashin ayyukan yi, za mu yi tunanin kamfanoni masu zaman kansu za su iya biya, sai kuma su zo su gaza, abin da za su yi na gaba shi ne korar ma’aikata.’

Yajin aiki: Gwamnati ta gargadi ma’aikata

Mun ruwaito muku cewa gwamnatin tarayya ta gargadi ma’aikata yayin da aka fara yajin aikin sai baba ta gani biyon bayan gaza cimma matsaya kan mafi karancin albashi.

Ministan shari'a, Lateef Fagbemi SAN ne ya yi gargadin, tare da yi wa ma’aikatan barazanar za su iya fuskantar hukuncin dauri a gidan tarbiyya da gyaran hali.

Asali: Legit.ng

People are also reading